✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar Wanzamai ta yi wa yara 500 shayi kyauta a Daura

kungiyar Wanzamai ta Masarautar Daura ta yi wa yara guda 500 shayi kyauta ranar Alhamis din makon jiya.Kamar yadda Sarkin Askan Masarautar Alhaji Usman Iliyasu…

kungiyar Wanzamai ta Masarautar Daura ta yi wa yara guda 500 shayi kyauta ranar Alhamis din makon jiya.
Kamar yadda Sarkin Askan Masarautar Alhaji Usman Iliyasu wanda ya samu wakilcin Malam Musa Wanzan ya bayyana cewa sun dade suna wannan yunkuri na yiwa yara marayu da wadanda ba su da galihu da ke yankin masarautar wannan shayi kyauta, amma ba su samu damar aiwatar da hakan ba sai a wannan lokacin.
Sarkin ya ce “wannan shi ne na farko a tarihin masarautar. Kuma mun aiwatar aikin shayin ne daidai lokacin bayan sun lura da irin yanayin da ake ciki. Mun fara tattauna da jama’armu don ganin cewa wace irin gudunmuwa za mu bayar ta fuskar sana’armu don tallafa wa masarautar. Daga nan muka yanke shawarar yin wannan shayi ga yaran da suka rasa mahaifansu ko wadanda mahaifan nasu ba su da halin yi masu saboda hali na rayuwar yau da kullum.  Abin ba ya tsaya a wannan karon ba ne kawai, za mu ci gaba da binciko irin wadannan yara. Mun dauki wadannan 500 ne domin ya zamo mabudin wannan tallafi ga wadannan yara mabukata kuma kyauta.”
Ya kara da cewa sun tattara wadannan yara ne ta hanyar Magaddai da Masu Unguwanni sannan kungiyar ta bayar da takardar ga duk yaron da za a yi wa shayin.
Da yake karin haske a kan gudunmuwar, Sakataren kungiyar Malam Usman Abba ya ce  sun dauki yara 200 daga karamar hukumar Daura yayin da suka raba sauran yara 300 a tsakanin kananan hukumomin Baure da Mai Aduwa da Sandamu da kuma Zango.
Ya ce kungiyar tana da mambobi fiye da 200. Hakazalika, ya ce suna tafiya da zamani ta hanyar tuntubar ma’aikatar kiwon lafiya ta yanki domin samun shawarwari musamman a kan yaki da cutar mai karya garguwar jiki wadda ake cewa sana’arsu ta wanzanci na daya daga cikin masu yada ta.
Daga nan ne sakataren ya bukaci gwamnati da ta bai wa wannan kungiya kulawa ta musamman tare da ba ta wasu kayan aiki musamman irin na zamani don ci gaban wannan kungiya da sana’ar baki daya.
Hakazalika, Shugaban Sashen jin Dadi da Walwala Mai Kula da Yankin Daura Alhaji Abdurrashid Rabe wanda ya yi magana a madadin iyayen yaran ya nuna farin cikinsa a kan irin wannan aiki da wannan kungiya ta yi.