✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Tarayyar Turai ta kaddamar da shirin bunkasa aikin rigakafi

Kungiyar Tarayyar Turai ta taimakawa Najeriya da kayyakin gudanar da aikin kiwon lafiya a jihohi 23 musamman don yakar cututtuka da za a iya magancesu…

Kungiyar Tarayyar Turai ta taimakawa Najeriya da kayyakin gudanar da aikin kiwon lafiya a jihohi 23 musamman don yakar cututtuka da za a iya magancesu ta hanyar rigakafi da kuma sauran lamura da suka shafi mata da kananan yara. 

Jakadan kungiyar don aiki na musamman a Najeriya da sauran kashashen yammacin Afirka Mista Ketil Karlsen ne ya bayyana hakan a yayin kaddamar da shirin a kauyen Gui da ke karamar hukumar birnin da kewaye na Abuja wato AMAC, a ranar Juma’ar da ta gabata inda a ka raba motocin hilos 29 ga jihohin da kuma yankin birniin tarayya Abuja, da su ka samu wakilcin kwamishinoninsu na kiwon lafiiya.

 Jakadan ya ce kungiyar ta kashe adadin Naira biliyan 3.8 bil wajen samar da motocin da za a yi amfanin da su wajen safaran magungunan rigakafi a jihohin da su ka amfana, sai kuma sabunta kananan cibiyoyin kiwon lafiya a jihohin, ko kuma ginawa a wani wajen, da aikin dakunan ajiya na sanyi, da samar da na’urar ajiya na sanyi mai amfani da hasken rana wanda za a fara aiki da su.

Hakanan kuma ya ce shirin wanda yarjejeniiya ce a tsakanin kungiyar da ma’aikatar tsare-tsare da kasafin kudi na Najeiriya, wanda aka sake jaddadawa a shekarar 2011 zuwa 2018, ya kuma bada horo ga ma’aikatan rigakafi 1,400, kamar yadda ya kashe adadin naira miliyan dubu 7 da dari biyu don yakar cutar poliyo a shekara ta 2001 wanda ya hada harda wasu jihohin na daban.

A yayin taron wanda ya samu halarcin karamin ministan lafiya na Najeriya Dokta Emmanuel Osage, da shugaban karamar hukumar birni da kewaye na Abuja malam Abdullahi Adamu kandido, da kuma wakilcin ministan birnin Abuja malam Muhammad Musa Bello da kuma mai martaba sarkin Jiwa Alhaji Idris Musa da takwaransa na Garki wato sapayen Garki Alhaji Usman Nga Kupi, an kaddamar da cibiiyar kiwon lafiya na kauyen da kungiyar ta sabunta tare da samar masa kayayyakin gudanar da aiki da kuma gina rijyar burtsaisi a wajen don asibitin da kuma al’ummar kauyen.

karamar hukumar AMAC ta taimaka da sake aikin share hanyar kasa da ya taso daga babban titin filin saukan jirgi na Abuja zuwa kauyen. Aminiya ta gano cewa jihohn da ba su amfana a wannan shirin ba sun hada da: Adamawa da Bayalsa da Benuwai da Borno da Delta Ekiti da Enugu da Imo da Nassarawa da Neja da Ondo da Oyo da kuma Taraba inda wata majya ta ce wadannan jihohn sun amfana a tallafi na baya ko kuma su na dakarancincin matsalolin. babban daraktan hukumar kula da kiwon lafiya a mataki na farko dokta Faisal Shu’aib wanda ya bayyana matukar farincikin Najeriya da daukin, ya ce hukumarsu za ta tabbatar da cewa wadanda a ka yi shirin dominsu sun amfana da shi.