✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kungiyar Tarayyar Afirka ta zabi sabon shugaba

Shugabannin sun yi kakkausar suka kan jerin juyin mulkin da aka yi a baya-bayan nan.

A yayin taron kolinta karo na 35 da ta gudanar a karshen mako, kungiyar Tarayyar Afirka wato AU, ta zabi Shugaban kasar Senegal wanda zai jagorance ta na wani sabon wa’adi.

Kungiyar Tarayyar Afirka ta zabi shugaban kasar Senegal Macky Sall, a matsayin sabon shugabanta na wa’adin shekara guda.

Kungiyar ta zabi shugaban na Senegal ne yayin taron da ta gudanar a shelkwatarta da ke Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, bayan karewar wa’adin Felix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Congo.

A karshen taron koli da suka kammala a ranar Lahadi, shugabannin sun yi kakkausar suka kan jerin juyin mulkin da aka yi a baya-bayan nan a wasu kasashen nahiyar wanda ya janyo kungiyar ta dakatar da kasashen daga wakilci a cikinta.

Shugabannin sun kuma dakatar da muhawara a game da wakilcin kasar Isra’ila a matsayin ’yar kallo a kungiyar, wanda shugaban hukumar gudanarwarta Moussa Faki Mahamat, ya amince da batun cikin watan Yulin bara.