A yayin taron kolinta karo na 35 da ta gudanar a karshen mako, kungiyar Tarayyar Afirka wato AU, ta zabi Shugaban kasar Senegal wanda zai jagorance ta na wani sabon wa’adi.
Kungiyar Tarayyar Afirka ta zabi shugaban kasar Senegal Macky Sall, a matsayin sabon shugabanta na wa’adin shekara guda.
Kungiyar ta zabi shugaban na Senegal ne yayin taron da ta gudanar a shelkwatarta da ke Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, bayan karewar wa’adin Felix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Congo.
A karshen taron koli da suka kammala a ranar Lahadi, shugabannin sun yi kakkausar suka kan jerin juyin mulkin da aka yi a baya-bayan nan a wasu kasashen nahiyar wanda ya janyo kungiyar ta dakatar da kasashen daga wakilci a cikinta.
Shugabannin sun kuma dakatar da muhawara a game da wakilcin kasar Isra’ila a matsayin ’yar kallo a kungiyar, wanda shugaban hukumar gudanarwarta Moussa Faki Mahamat, ya amince da batun cikin watan Yulin bara.