kungiyar Bunkasa Ci Gaban Kudancin Kaduna (SOKADEF), ta koya wa mata da matasa fiye da dubu daya daga kananan hukumomi takwas na yankin sana’o’in hannu.
An gudanar da bikin yaye wadanda suka yi kammala koyon sana’o’in ne a dakin taro na New Choice da ke garin Kafanchan a karshen mako.
Shugaban kungiyar, Dokta Daniel Rikichi Kajang, ya bayyana wa taron cewa burinsa shi ne samar wa matasa miliyan daya da ayyukan dogaro da kai a yankin.
Ya ce manufar kungiyarsa ita ce taimaka wa matasa wajen tabbatar da mafarkinsu na zamowa daga cikin wadanda jama’a za su amfana da su nan gaba ta hanyar dogaro da kai.
“Ayyukanmu suna tafiya kafada-da-kafada da manufofin gwamnati wajen samar da aikin yi ga matasa da samar da tsaro da zaman lafiya. Ganin irin rikice-rikicen da suka dabaibaye yankin Kudancin Kaduna da muka lura suna da alaka da talauci da rashin aikin yi ya sa kungiyarmu, tare da hadin gwiwar Hukumar Samar da Aikin yi ta kasa (NDE), ta shirya horar da matasan ayyukan yi. Mutum baya bukatar sai ya zama ma’aikacin gwamnati ko dan siyasa kafin ya amfanar da jama’a,” inji shi. Sai ya bukaci matasasu yi watsi da “Harkokin shaye-shaye da ayyukan batagari su rungumi gobensu a yau,” inji shi.
A jawabin Shugaban Taron, Farfesa Ayuba Kura, ya ce Allah Ya albarkaci Kudancin Kaduna da kasar noma da sauran albarkatun kasa, amma rashin masu kishin yankin daga cikinsu ya sanya yankin ya zama koma-baya, inda ya yi kira ga masu hannu da shuni su yi koyi da Dokta Rikichi wajen koyarwa tare da samar wa matasan yankin abubuwan dogaro da kai ta yadda za su rage dogaro da aikin gwamnati.
Dukan wadanda suka gabatar da jawabi sun jinjina wa kungiyar SOKADEF bisa nuna kishin yankin, tare da yin kira ga wadanda suka amfana su rike sana’o’insu da kyau kuma su koyar da na bayansu domin rage masu zaman kashe wando a cikin al’umma.
Sana’o’in da aka koya musu sun hada da walda da yin takalma da dinki da kafinta da nada setilayit da daukar hoto da aikin kwamfuta da kiwon kifi da na kaji da sauransu.
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai tsohon Mataimakin Hukumar Samar da Aikin yi ta kasa (NDE), Mista Eli da Uwargidan Mataimakin Gwamnan Jihar Kaduna, Misis Ladi Barnabas Bala Banted da sarakunan gargajiya daga yankin da wakilan kungiyoyin JNI da CAN.