✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar Red Cross ta horar da ’yan agaji a Bauchi

A ranar Talatar makon jiya ne kungiyar ba da agaji ta kasa-da kasa Red Cross reshen Jihar Bauchi ta horar da ’yan agajin kungiyar Izala…

A ranar Talatar makon jiya ne kungiyar ba da agaji ta kasa-da kasa Red Cross reshen Jihar Bauchi ta horar da ’yan agajin kungiyar Izala dabarun tallafa wa marasa lafiya idan wata masifa ta auku.
Shugaban kungiyar Izala reshen Jihar Bauchi Alhaji Muhammed Inuwa dan Asabe ya bayyana cewa wadanda suka samu horon sun hada da ’yan agaji wadanda suka fito daga jihohin da dama. Alhaji Inuwa ya kara da cewa duk shekara kungiyar Red Cross reshen Jihar Bauchi tana shirya taron.
Daga bisani shugaban ’yan agaji na kasa Imam Mustapha Sitti ya raba satifiket ga wasu daga cikin ‘yan agaji da suka yi kwazo a lokacin taron bitar na kwanaki uku da aka gudanar a jihar.
Daga nan ya bayyana wa wakilinmu cewa yana fatan wadanda suka samu horon idan sun koma jihohinsu za su fadakar da sauran ’yan agaji dabarun tallafa wa marasa lafiya idan wani Iftila’i ya faru.