kungiyar Masu Kiwon Tsuntsaye ta kasa (PAN) reshen Jihar Kano ta koka tare da nuna damuwarta game da yadda cutar murar tsuntsaye ke yaduwa kamar wutar daji.
Mataimakin Sakataren kungiyar Umar Usman Kibiya ya ce masu noman tsuntsayen na fuskantar babbar barazana game da kasuwancinsu. “A yanzu haka mambobinsu sun yi asarar fiye da Niara miliyan 500 a cikin watanni biyu,” inji shi.
Ya bayyana cewa abin da ya fara a kananan hukumomi uku a yanzu ya watsu zuwa kananan hukumomi 11, inda gonaki fiye da 57 suka kamu. Har ila yau, ya ce tun bayan dawowar cutar a watan Disambar bara kimanin tsuntsaye dubu 300 aka yi asararsu.
Ya ce “Idan har za a bar masu noman tsuntsaye su ci gaba da gudanar da sana’arsu a bisa wasu sharudda to babu shakka za a ci gaba da samun yaduwar wadannan abubuwa, hakan ya sa muke kira ga gwamnatin jiha don su dauki matakin hana bubbude kananan wuraren kiwon dabbobi,” inji shi.
Har ila yau, ya ce ya dace a farfado da shirin nan na bayar da shawarwari a matakan kananan hukumomi 44 da ke fadin jihar don a rika samun bayanai ta yadda za a dauki matakin da ya dace wajen maganin irin wadanan abubuwa.
Daraktan bangaren kula da dabbobi na ma’aikatar Ayyukan Gona ta Jihar, Dokta Bawa Shehu ya bayyana cewa zuwa yanzu an samu fiye da tsuntsaye dubu 330 wadanda suka harbu da wannan cutar. Hakazalika, ya bayyana cewa suna fuskantar matsaloli wajen gudanar da aikin magance wanann annobar saboda yankewar kayan aiki da ake kira da PPE wanda kuma ba a samunsu ko a kasuwannin da ke fadin kasar nan.
A karshe daraktan ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta taimaka wa jihar don ganin an yi maganin yaduwar wannan annobar.
kungiyar PAN ta koka game da cutar murar tsuntsaye
kungiyar Masu Kiwon Tsuntsaye ta kasa (PAN) reshen Jihar Kano ta koka tare da nuna damuwarta game da yadda cutar murar tsuntsaye ke yaduwa kamar…