kungiyar ‘yan jarida wato (NUJ) reshen Jihar Katsina ta fito da wani shirin tattaunawa da jami’an gwamnatin jihar domin bayyana wa al’ummar irin halin da gwamnati take ciki.
Shugaban kungiyar Alhaji Buhari Mamman Daura ya shaida wa Gwamna Masari a lokacin bikin kaddamar da wannan shirin, inda ya ce sun bullo da tsarin ne domin ba gwamnatin da sassanta damar bayyana wa al’ummar jihar irin halin da suke ciki ta fuskar ayyukan ci gaba ko inda suka samu wata matsala.
Ya ce, “irin damar da wannan gwamnati ta bayar ga al’ummar jihar ta fadin albarkacin bakinsu a kafofin yada labarai mallakar gwamnatin jihar ba tare da nuna bambancin siyasa ko akida ba, sabanin gwamnatin da ta shude inda ta mayar da kafofin tamkar ‘yan amshin shata.” Har ila yau, ya ce, dama ‘yan jarida su ne kashin bayan ci gaba kowace al’umma ba wai ga gwamnati ba musamman ta fuskar ilimantarwa da fadakarwa da sauransu.
Shugaban Kwamitin yin wannan tattaunawar, Alhaji Abdulhamid Sabo wanda kuma shi ne wakilin jaridar Blueprint, ya ce sun zabo mambobin wannan kwamiti ne daga kafofin yada labarai mallakar gwamnati da kuma wadanda suke masu zaman kansu da kuma bangaren wakillan sauran jaridun da ke cikin jahar domin su tsaya tare da aiwatar da wannan ganawa domin tattaunawa da yankunan gwamnatin jihar wanda suka fara tun daga shi ofishin gwamnan.
kungiyar NUJ ta bullo da shirin ganawa da jami’an gwamnati
kungiyar ‘yan jarida wato (NUJ) reshen Jihar Katsina ta fito da wani shirin tattaunawa da jami’an gwamnatin jihar domin bayyana wa al’ummar irin halin da…