✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar NUJ reshen Bauchi ta yi maraba da sabbin shugabanninta na kasa

kungiyar ’Yan Jarida ta kasa (NUJ) reshen Jihar Bauchi ta jinjina wa sabbin shugabannin uwar kungiyar ta kasa da aka zaba a karshen makon jiya,…

kungiyar ’Yan Jarida ta kasa (NUJ) reshen Jihar Bauchi ta jinjina wa sabbin shugabannin uwar kungiyar ta kasa da aka zaba a karshen makon jiya, a Abuja.

A wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Bauchi, sakataren kungiyar Alhaji Bashir Idris ya bayyana, “cewa reshen kungiyar na jiha yana fatar alheri ga wadanda aka zaba, Allah Ya ba su damar sauke nauyin da aka dora musu,” inji shi.
Sakataren ya kara da cewa: “Muna mika godiyarmu a madadin ‘ya’yan kungiyar na Jihar Bauchi bisa yadda aka zabi Alhaji Murtari Gidado a matsayin mataimakin shugaban kungiyar na kasa. Har ila yau, muna fatan zai ci gaba da ba da dukkan gudunmawa ga daukacin ‘yan jaridar yankin Arewa-maso-Gabas da ma Najeriya baki daya,” inji shi.
A ranar Asabar da ta gabata ne uwar kungiyar ta kasa ta zabi Mista Abdulwaheed Odusile, wanda yake aiki da jaridar The Nation a matsayin sabon shugaba. Ya samu galaba ne da kuri’u 354, inda ya doke abokin takararsa Mista Rotimi Obamuwagun mai kuri’u 333. Sabon shugaban ya gaji Malam Garba Mohammed ne.