Kungiyar Masana Madinai da Albarkatun Kasa wacce ake kira (NMGS) ta yi kira ga membobinta su dakatar da ayyukansu har sai an ceto membobinsu da Kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da su.
Kungiyar ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta shiga tattaunawa da Kungiyar Boko Haram don ceto membobin kungiyar.
Kungiyar ta yi kiran ne yayin da take ganawa da manema labarai a garin Ilorin da ke jihar Kwara kan kisan gillar da Kungiyar Boko Haram ta yi wa wasu membinta.
Da yake jawabi ga manema labarai a jiya, Shugaban Kungiyar (NMGS), Farfesa Silas Sunday ya bayyana cewa ba sun kira taron ba ne don su soki gwamnati kan kokarin take yi kan lamarin sai don su bayyana kisan gillar da Kungiyar Boko Haram ta yi wa membobinsu yayin da suke kan aiki.