kungiyar Masu Makarantun Kudi ta kasa wacce a takaice ake kira NAPPS, ta goyi bayan kudin da mambobinta suke karba a makarantunsu daga hannun iyayen yara.
kungiyar ta ce suna yin amfanin da kudin ne wajen biyan albashi da tafiyar da harkokin makarantunsu.
Shugabar kungiyar ta kasa, Dokta Sally Adukwu Bolujoko ita ce ta yi furucin yayin da take tattaunawa da Aminiya a Abuja a karshen makon da ya gabata.
“Ai ba wani kudin kirki muke karba ba. Kudin da muke karba muna yin amfani da su ne wajen daukar dawainiyar dimbin ma’aikatan da ke karkashinmu tare da biyan haraji ga gwamnati da kuma sauran matsaloli na makarantunmu,” inji ta.
Ta bayyana cewa kungiyarsu tana bayar da gudunmawa sosai dangane da ci gaban kasar nan.
A cewarta mambobin kungiyar suke samar da ayyukan yi ga dimbin jama’a da suke neman aikin yi.
Har ila yau, ta ce mambobin kungiyar sun kasance masu kishin kasa saboda dimbin harajin da suke biyan gwamnati.
Sai dai kuma ta koka kan yawan harajin da gwamnati ke karba a wurinsu kodayaushe.
Daga nan sai ta yaba wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda muhimmancin da yake bai wa bangaren ilimi.
Ta ce “Shugaban kasa ya cancanci yabo saboda yadda yake bai wa sashen ilimi muhimmanci. Yanzu ka duba yadda ya bai wa sashen ilimi kaso mai tsoka. Ka ga wannan abin a yaba ne kuma abin son barka ne. Saboda haka muna goyon baya tare da yin addu’ar samun nasara,” inji ta.
Ta yi kira ga gwamnati ta kawo wa kungiyar dauki ta hanyar tallafawa mambobin kungiyar tare da ba su lamuni wanda babu kudin ruwa a cikinsa.
Ta bayyana cewa matakan da shugaban kasa yake dauka kan ilimi zai taimaka mutuka wajen maganin matsalolin da ke addabar ilimi a kasar nan.
Sai dai kuma ta yi kira ga jama’a su bai wa shugaban kasa goyon baya don cimma burin da ya sanya a gaba na gyara kasar nan.