✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar nakasassu ta Bauchi ta samu tallafin kayan abinci

kungiyar nakasassu ta Jihar Bauchi ta karbi agajin kayan abinci daga Gwamna Malam Isa Yuguda na Jihar Bauchi don shirin shiga azumin watan Ramadan, kamar…

kungiyar nakasassu ta Jihar Bauchi ta karbi agajin kayan abinci daga Gwamna Malam Isa Yuguda na Jihar Bauchi don shirin shiga azumin watan Ramadan, kamar yadda aka saba tallafa musu.
Shugaban gamayyar kungiyoyin ’yan kasuwa na Jihar Bauchi, Alhaji Salisu Garba Maisuga shi ne ya mika kayayyakin ga sarakunan nakasassu na jihar, ranar Lahadin da ta gabata, inda cikin jawabinsa ya bayyana gwamnatin jihar ta Bauchi ta ba shi amanar raba musu kayan abincin, kamar yadda aka saba daga lokaci zuwa lokaci, a fili don kowa ya san abin da aka ba shi.
Kayan abincin sun kunshi buhunan masara 4,100; shinkafa 2,000; gero 2,300 da kuma sukari 1,000, wadanda Alhaji Salisu ya yi fatar za a raba su tsakanin nakasassun yadda ya kamata cikin adalci,  yadda za su gamsu da rabon da aka yi.
Cikin jawabinsa a yayin amsar tallafin, Sarkin Makafin Bauchi, Alhaji Abdullahi Jibrin ya yabi taimakon da ake wa nakasassun, lamarin da ya sa kashi bakwai cikin goma na musakan Jihar Bauchi sun daina bara, kuma ya yi na’am da aka sanya rabon kayan ta hannun shugaban Gamayyar kungiyoyin ’yan kasuwa, Alhaji Salisu Garba, wanda ya ce a wasu lokuta ko tallafin gwamnati bai iso ba, yana taimaka musu.
Ya kirayi sauran gwamnoni a Najeriya su yi koyi da gwamnatin Jihar Bauchi wajen ciyar da miskinai fisabilillahi, lamarin da ke kawo zaman lafiya a kasa da kuma kawar da talauci da bala’i da cututtuka saboda addu’ar nakasassu da talakawa.
Ya ce kwamitoci hudu za su raba kayan ga makafi da kutare da guragu da kurame da iyalansu, ta yadda kowa zai gamsu da rabon gwargwadon yawan iyalansa.
Daga karshe ya yi addu’ar Allah Ya kawo karshen matsalar da ake fama da ita, a kasa da kuma musamman a jihohin Arewa.
Shi ma Sarkin Guragu, Malam Abubakar Bello ya gode game da alhairan da Gwamna Yuguda da matarsa Hauwa Biodun ke ba su na tallafi duk wata shida, lamarin da ke rage zafin fita yin barar neman abin da za su ci, kuma ya sa guragun da ke Kudu sun dawo gida sun zauna.
Sarkin Kutare Zakari Ya’u Bala Usman shi ma ya gode game da tallafin, tare da bayyana kiran da ’yan kwamitin rabon suka na kowa ya je ya karbi rabons don kada a samu korafi don a gaban kowa za a yi shi. Ya yi fatar musakan za su ci gaba da yi wa kasa da gwamnati addu’ar samun zaman lafiya da ingantuwar lamurra.
Ali Abdullahi Shongo, shi ne shugaban hadaddiyar kungiyar nakasassu ta Jihar Bauchi ya ce suna yi wa gwamna addu’a, saboda a zatonsu duk Najeriya babu gwamnatin da ke irin wannan ga nakasassun sai a jihar. Ya shawarci shugabannin da a natsu wajen ganin an raba kayan ta yadda kowa zai gamsu, kuma ya bukaci kowa ya himmatu wajen neman sana’a don kare mutuncinsa da iyalansa, ya nisanci yawon bara saboda wahala da kaskanci da ke cikinta.