✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar nakasassu a Jihar Yobe ta roki gwamnati kan tallafin SURE-P

kungiyar nakasassu ta Jihar Yobe ta nemi gwamnatin jihar ta sadaukar mata da kashi 20 cikin 100 na tallafin shirin nan na SURE-P, don amfanin…

kungiyar nakasassu ta Jihar Yobe ta nemi gwamnatin jihar ta sadaukar mata da kashi 20 cikin 100 na tallafin shirin nan na SURE-P, don amfanin mambobinsu ta yadda za su san su ma ana damawa da su a harkokin rayuwar yau da kullum a matsayinsu na ’yan kasa.
Bayanin hakan dai ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar, Komred Muhammad Abba Isa, a yayin da suka kai ziyarar giramamawa ga sakataren gwamnatin jihar, Injiniya Baba Goni Machina a ofishinsa da ke garin Damaturu. Haka nan sun nemi gwamnatin ta gyara musu cibiyoyin kula da nakasassu guda 7 da ake da su a jihar don samar musu abin yi don rage yawaitar tafiye-tafiyensu zuwa jihohi makwabtansu irin su Bauchi da Filato don neman abinci.
Shugaban ya kara da cewar, “Muna kuma rokon gwamnati ta rika ware mana kasonmu daga cikin irin kayayyakin masarufin da take samarwa a yayin bukukuwan sallah da kuma ba mu kujeru don gudanar da aikin hajji. Sannan ta rika sa mambobinmu a duk wani matsayi irin na siyasa da take bayarwa ga jama’a don al’ummominmu su  ma su amfana”.
Daga nan kuma ya roki gwamnati ta taimaka ta kafa musu wata hukuma ta musamman domin ta kula da harkokinsu, wanda yin hakan zai taimaka matuka wajen ganin suna magana da murya daya.
Da yake mayar da jawabi, sakataren gwamnati, Injiniya Baba Goni Machina, wanda babban sakatare a kan harkokin siyasa, Malam Hassan Gana ya wakilta, ya bada tabbaci ga shugabannin kungiyar cewar, wadannan koke-koke nasu za a tura su gaban mahukunta don yin wani abu a kai.