Kungiyar ci gaban Matasa ta Nagarta da ke Jihar Kano ta nemi hadin kan Kamfanin Media Trust da ke buga jaridun Aminiya da Daily Trust wajen ganin an kawo karshen harkar shaye-shayen miyagun kwayoyi da ya addabi al’ummar jihar.
Shugaban Kungiyar Aminu Idris ne ya yi wannan kira a lokacin da tawagar kungiyar suka kawo ziyara ofishin kamfanin da ke Jihar Kano.
Malam Aminu ya bayyana cewa duba da irin muhimmancin da kafar watsa labarai ke da shi ya zama dole kungiyar ta hada kai da kamfanin wajen tallata wa al’umma manufofin kungiyar da kuma irin nasarari da kalubalen da kungiyar ke fuskanta.
Malam Aminu Idris ya bayyana cewa kungiyar tasu na kokarin sama wa masu shaye-shayen miyagun kwayoyi sana’a ta yadda za su dogara da kansu tare da fita daga harkar shaye-shayen nan kwata-kwata “Abin da muke yi shi ne muna nemo irin wadanda suka fada wannan harka ta shaye-shaye muna zama da su inda muke nuna musu illar da ke cikin harka har sai sun amince za su bari. Daga nan sai mu sama musu abin yi. Domin mun fahimci cewa rashin aikin yi na taka muhimmiyar rawa wajen ta’azzara harkar shaye-shayen a tsakanin matasa.
Malam Aminu ya yi kira ga gwamnati da hukumomin da abin ya shafa da su yi kokarin daukar matakin hana shigowa da muggan kwayoyin a maimakon mayar da hankali kacokan akan kokarin hana shan kwayoyin.
Kungiyar ta sha alwashin kawo karshen harkar shaye-shaye a jihar cikin wata shida rak matukar gwamnati za ta tallafa wa kokarin kungiyar da duk abubuwan da take bukata
Da yake mayar da jawabi Malam Ibrahim Musa Giginyu a madadin Manajan Shiyya ya bayyana cewa Kamfanin na Media Trust a shirye yake ya bayar da gudummawarsa a kowane lamari da ya shafi ci gaban al’umma, don haka kamfanin zai ba kungiyar gudummawar da take bukata don cim ma muradinta.