A ranar Asabar da ta gabata ne kungiyar Mata ’Yan uwa Musulmi ta kasa wato Muslim Sisters Organisation (MSO) reshen Jihar Yobe ta horar da marayu da wasu yara da ke dauke da cutar kanjamau su fiye da 40 sana’o’i daban-daban don dogaro da kansu.
Bayanin hakan dai ya fito ne daga bakin jagorar shirin kuma Amira ta kungiyar a jihar Hajiya Gambo Aji Suleiman a zantawarta da Aminiya bayan kaddamar da bikin ba da takardar shaidar kammala horon ga wadanda suka samu horon a garin Damaturu.
Ta ci gaba da cewa wannan kungiyarsu tana kan gaba a jerin kungiyoyi da ke samar da tallafi musamman wajen abin da ya shafi cutar kanjamau a Jihar Yobe.
Hajiya Gambo ta kara da cewar akalla matasa kusan marayu 220 da masu dauke da cutar kanjamau ke amfana daga tallafin da kungiyar ke samarwa musamman ta fuskoki irinsu kayayyakin koyon karatu da rubutu ga dalibai a fannoni daban-daban na ilimi da kuma abincin da ke kara kuzari ga yaran da ba su isashasshen abinci a jikinsu da sauransu.
Don haka ta yi kira ga wadanda suka ci gajiyar wannan horo da su yi amfani da horon da suka samu da kuma kayayyakin da aka ba su da suka shafi kekunan dinki da kayayyakin yin sabulai da sauransu.
Wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar wannan horo Falmata Sadik da kuma Hassan Mustapha a tattaunawarsu da Aminiya sun yi godiya ga kungiyardangane da wannan horo da tallafi da ta ba su, inda suka nemi daidaikun mutane da kungiyoyi da su yi koyi da irin wannan yunkurin.
kungiyar MSO ta bai wa marayu 40 horo a Damaturu
A ranar Asabar da ta gabata ne kungiyar Mata ’Yan uwa Musulmi ta kasa wato Muslim Sisters Organisation (MSO) reshen Jihar Yobe ta horar da…