✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar Miyetti Allah ta kafa kwamitin samar da tsaro a Nasarawa

kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah Kautal Hore ta yi kira ga Onah na Toto da ke karamar hukumar Toto ta Jihar Nasarawa, Alhaji Muhammad…

kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah Kautal Hore ta yi kira ga Onah na Toto da ke karamar hukumar Toto ta Jihar Nasarawa, Alhaji Muhammad Umar Azaki da ya tallafa wajen kyautata zamantakewa a tsakanin mambobinsu da sauran jama’ar yankin don magance rigingimu da kuma samuwar ci gaban jama’ar baki daya.
Shugaban kungiyar reshen Jihar Nasarawa Alhaji Gidado Idris ne ya bayyana bukatar a yayin kaddamar da kwamitin samar da tsaro na kungiyar a yankin inda ta bashi matsayin uban kungiya.
Alhaji Gidado Idris wanda ya bayyana farin cikinsa na halartan taron da daukacin masu rike da sarautu na yankin su ka yi, ya ce sun kafa kwamitin ne don zakulo vata-gari a cikin al’ummansu don ladabtar da su da kuma tabbar da cewa ana bin doka a tsakaninsu da manoma. Sakataren kungiyar reshen Jihar Nasarawa, Malam Ja’afaru Liman ya bukaci manoma da suka halarci taron da su gabatar da duk wani korafi da suke da shi ga kungiyar don daukan matakin gyara.
Wani manomi da ya yi jawabi a madadin sarkin manoman yankin mai suna Malam Ahmadu Abdu, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta hanzarta daukan matakan hana kutsen dabbobi a cikin gonaki musamman a yayin girbi, inda ya yi hasashen cewa a kwai yiwuwar kazantar matsalar a bana idan ba a dauki matakin gaggawa ba a sakamakon karuwan sabbin gonaki da ya ce an samu a wannan damina saboda tsadan abinci.
Da ya ke maida jawabi Onah na Toto Alhaji Muhammad Umar Azaki ya bayyana taron a matsayin babban abin farin ciki a gareshi bayan zamowansa Basarake, ya ce a shirye yake ya ba da duk wata gudunmawa da zai kawo zaman lafiya da kuma ci gaban yankin a kowane lokaci. An bayyana Alhaji Faruk Ardo Toto a matsayin jagoran kungiyar a yankin. Taron ya samu halarcin jagoran babban ofishin ’yan sanda (DPO) na Toto da kuma takwaransa a vangaren jami’an tsaro na farin kaya wato SSS.