Akalla mata marasa galihu 1,500 ne kungiyar Mata Masu Da’awah ta kasar nan reshen Jihar Neja ke fatan tallafa musu da abin da za su ci kafin karshen watan azumin Ramadan, kamar yadda shugabar kungiyar ta bayyana wa Aminiya.
Taimakon ya kunshi hatsin da za su rika sarrafawa domin samun abin da za su rika kai wa bakin salati.
Wadanda kungiyar suka mika wa goron gayyata kamar yadda suka saba duk shekara sun fito ne daga kananan hukumomin Chanchaga da Bosso da kuma Paikoro. Kodayake, galibinsu wadanda suka rasa mazansu ne.
Shugabar kungiyar Malama Rabi’atu danladi Makun yayin da take jawabi, ta bayyana farin cikinta ganin yadda ilahirin wadanda suka mika wa goron gayyata sun amsa kira suka halarci wurin.Daga nan ta tunawa matan cewa, “ya kamata su kara azama wurin gudanar da ayyukan bauta a wannan watan gwargwadon abin da ya samu ba tare da sun daura kansu a kan turbar abinda ya fi karfinsu ba.”
Shugabar ta ci gaba da cewa, “a duk shekara yadda muka saba banda mutanen da ke rukuninku wadanda mu kan samar wa hatsin masarufin da suka sawwaka da suka hada da dawa da masara da wake da shinkafa da kuma sikari, wadanda sukan biyo ta hannunmu daga hannun wasu bayin Allah da ba su so a ambaci sunayensu ba. Muna kuma kabe wasu cibiyoyi a wurare daban-daban da mukan samar da abincin bude baki,” inji ta.
Sakatariyar kungiyar Malama Aminah Abdul-Mumin ta ja hankalin matan ne da su kara hakuri da halin da suka samu kansu a ciki daga lokacin da Allah Ya karbi mazansu. Ta yi kira da su yi “la’akari da cewa ita kaddara tana daya daga cikin rukunan imani guda shida wadda kuma ta rabu biyu wato mai kyau da kishiyarta.”
Daga nan ta sake jan hankalinsu game da illolin da ke tattare da bin gidajen masu hannu da shuni suna neman su taimaka musu da abin da abinci. “Abin takaicin shi ne ganin yadda irin wadannan mutanen kan wulakanta wadannan matan da kan sha zafin rana da daga karshe akasari ba su saurarensu saboda haka yakamata su zama masu wadatar zuci a kowane lokaci. Da zarar sun rungumi wannan akidar Allah zai taimaka musu ta hanyoyi da dama wadanda ba su yi tsammani ba,” inji ta.
Malama Maimuna Ahmad wadda ta yi jawabin godiya a madadin matan da suka ci moriyar tallafin ta yi farin ciki da kyautar da suka samu a lokacin da ba su yi tsammani ba.