✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar masu ruwan leda ta nemi hadin kan ’ya’yanta

kungiyar masu sayar da ruwan leda da, a kwanakin baya, suka mayar da farashin ruwan ya koma Naira goma a maimakon Naira biyar da ake…

kungiyar masu sayar da ruwan leda da, a kwanakin baya, suka mayar da farashin ruwan ya koma Naira goma a maimakon Naira biyar da ake sayar da shi a can baya, sannan kuma daga baya ta janye karin, yanzu ta bukaci dukkan mambobinta su baiwa uwar kungiyar cikakken hadin kan da ya kamata.
Shugaban kungiyar, reshen Jihar Kano, Alhaji Salisu Sani Zage, ya yi kiran haka a yayin wani taro na kungiyar ranar Asabar, a dakin taro na Sakatariyar Gwamnatin Tarayya da ke Kano. “Ana neman karin hadin kan ’yan kungiya wajen mayar da farashin ruwan a kan Naira sittin na babbar jaka ta ledojin ruwan, a maimakon Naira tamanin, wato Naira biyar ke nan kowace karamar jaka. Da farko mun yi karin farashin ne saboda tashin farashin leda da sauran sinadarai na tace ruwan, amma a saboda kiran da gwamnatin Jihar Kano ta yi mana, mun janye karin, domin mu ma mu bayar da gudummawarmu wajen taimaka wa jama’a”, inji shi.
Ya musanta cewa ba sun kara kudin ne don koyi da wasu jihohin da suke sayar da ruwan a kan wannan farashin ba, sai dai kawai don dalili na tsadar kayan sarrafa ruwan. Sannan kuma ya yi kira ga dukkanin masu wannan sana’ar da ba su yi rijista da kungiyar ba da su gaggauta yin rijistar, domin idan ba  su yi hakan ba, “to komai ya same su ko ya taso, babu ruwan kungiya da su”.
Daga nan kuma sai ya ja hankalin masu yin ha’inci wajen tsaftacewa da tace ruwan yanda ya kamata, wadanda ba su damu su sayar da ruwan a kan kowane farashi ba, su ji tsoron Allah. Haka nan ya bukaci gwamnati ta wadata musu masana’antu da wutar lantarki, domin hakan zai saukaka dawainiyar sarrafawar su sayar da kayansu bisa rahusa.