✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar masu faci a Jihar Nasarawa ta bukaci tallafin gwamnati

kungiyar masu faci a Jihar Nasarawa ta yi kira ga gwamnati ta tallafa wa ’ya’yanta da rance, musamman na kudi don inganta ayyukansu.Shugaban kungiyar na…

kungiyar masu faci a Jihar Nasarawa ta yi kira ga gwamnati ta tallafa wa ’ya’yanta da rance, musamman na kudi don inganta ayyukansu.
Shugaban kungiyar na jihar, Malam Abdulrahman Yukubu ne ya yi wannan roko a taron da kungiyar ta yi a karshen makon da ya gabata a Lafiya. Malam
Malam Abdulrahman ya bayyana cewa kungiyar a halin yanzu tana shan wahala sosai wajen gudanar da ayyukanta, idan aka kwatanta da sauran sana’o’i a jihar, saboda rashin kudaden da za su sayi kayayyakin aiki na zamani. Saboda haka, sai ya yi kira ga gwamnatin jihar ta kawo musu dauki cikin hanzari domin su samu damar yin gogayya da sauran takwarorinsu.
Malam Abdulrahman ya kuma yi kira ga ’ya’yan kungiyar su kasance masu bin doka da oda tare da bayar da cikakken goyon bayansu ga manufofi da shirye-shiryen gwamnati mai ci yanzu a jihar, don samun ribar dimokuradiyya.
Taron, wanda ya sami halarcin ’ya’yan kungiyar da dama, daga ciki da  wajen Jihar Nasarawa, an gudanar da shi, musamman don a jaddada muhimmancin nuna kwazo da gaskiya da kuma rikon amana a yayin gudanar da sana’ar ta faci.  
Hakan kuwa ya bayyana ne jim kadan bayan taron, a yayin da Aminiya ta gana da shugaban kungiyar, Malam Abdulrahman don neman karin haske dangane da makasudin taron.