kungiyar Makera ta Jihar Filato da ke Titin Adebayo a cikin garin Jos ta koka kan rashin jari da matsalar wutar lantarki da kuma sauran kayayyakin aiki.
Shugaban kungiyar Alhaji Salisu Amadu ne ya mika kukan kungiyar ga gwamnatin Jihar Filato a lokacin da yake tattaunawa da wakilin Aminiya, a ranar Litinin da ta gabata.
Shugaba Salisu wanda ya bayyana cewa makerarsu ita ce ta daya a garin Jos, amma babu bunkasar a zo a gani da ta samu duk da cewa sun rika mika kokensu ga gwamnati don ta taimaka musu, inda a yanzu suke fama da rashin jari da kuma rashin wutar lantarki.
“Babban abin da yake ci mana tuwo a kwarya shi ne, gwamnatin da ta gabata da kuma ta yanzu ba ta san da mu ba. A zahirin gaskiya ba mu da isasshen jari, ga matsalar rashin wutar lantarki, ga shi gwamnati ba ta tallafa mana ba. A yanzu akwai aikin da muke yi a mako daya, amma idan har da muna da kayayyakin aiki, sannan a ce ana samun wutar lantarki, to aikin mako guda za mu iya yinsa a cikin wuni daya. Idan muka samu wutar lantarki komai zai zo mana cikin saukin,” inji shi.
Shugaban ya bayyana cewa sau daya suka taba samun tallafi, inda wani tsohon dan majalisar wakilai ya taimaka musu da kayayyakin aiki, inda a yanzu wadansu daga ciki suka lalace, amma ba su da halin gyarawa saboda suna bukatar canza wadansu kayayyakin, inda kayayyakin suke da tsada.
Shugaban ya kuma bayyana cewa ya shekara 35 a cikin kungiyar makera, kuma masana’antar kungiyar tana dauke da mutane fiye da 100.
“Mutane daga kananan hukumomin Filato da Kaduna da Bauchi suna zuwa sayen kayayyakin da muka kerawa irinsu garma da fatanya da lauje da magirbi da sauransu. Ka ga kuwa bai kamata a ce gwamnati ta manta da mu ba,” inji shi.
A cikin nasarorin da suka cimma har da kera wani inji mai suna ‘mai Fatari’ da kuma kera injunan nika da suka hada da na markade da nikan alabo da sauransu, sannan suna samar da karafan aikin kofa da kuma sauran karafa da masu walda suke zuwa saye a wurinsu.
A karshe ya bukaci ’yan kungiyar su ci gaba da bada hadin kai don kungiyar ta ci gaba da tsayawa da kafafunta.