Kungiyar Makafi ta kasa rashen Zariya ta Jihar Kaduna ta tallafa wa ’ya’yan kungiyar da kayayyakin karatu da tallafin karatu.
An gudanar da taron bayar da tallafin ne a dakin taro na Sashin Ilimi na Karamar Hukumar Zariya a ranar Talata.
Bako Mai jawabi Shugaban Kungiyar ’Yan Jarida rashen Gidan Rediyon Tarayya na Kaduna, Malam Salihu Ibrahim, ya jawo hankalin nakasassun da kada su gajiya wajen neman dogaro da kansu a fannin rayuwa.
Ya bayyana ilimi a matsayin ginshikin rayuwa wanda kowane mai rai yake bukata domin cimma burin rayuwa.
A cewarsa babu maraya sai rago don haka nakasa ba kasawa ce ba.
A sakon Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, wanda Ciroman Shantali ya wakilta ya bayyana cewa Masarautar Zazzau a shirye take ta tallafa wa nakasassu a duk lokacin da bukata ta taso.
Ya ce dukkan abin da ya gudana a wajen taron zai sanar da Mai martaba Sarkin Zazzau domin daukar matakin da ya dace.
Da yake jawabi, Shugaban Kungiyar Makafi ta Jihar Kaduna, Malam Haruna Ibrahim, ya roki Gwamnatin Jihar ta duba matsayin nakasassu da aka sallama daga aiki a jihar. Kuma ya ce a da Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi alkawarin cewa ba za ta dakatar da duk wani mai nau’in nakasa ba daga aiki; amma sai ga shi yanzu an sallami da dama daga cikinsu ba tare da an ba su hakkokinsu ba. Don haka ya roki gwamnatin ta duba koke-kokensu.