✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar makafi a Jihar Katsina ta zabi shugabanninta

kungiyar makafi ta Jihar Katsina ta zabi sababbin shugabannin da za su ja ragamarta. Zaben, wanda aka gudanar a ofishin jin dadi da walwala da…

kungiyar makafi ta Jihar Katsina ta zabi sababbin shugabannin da za su ja ragamarta.
Zaben, wanda aka gudanar a ofishin jin dadi da walwala da ke filin Samji a garin Katsina a ranar Asabar,  ya samu halartar wakillai daga kananan hukumomi 33 daga cikin 34 da ke jihar. karamar Hukumar Mai’aduwa, wadda ke shiyyar Daura, ita ce kadai ba ta turo wakillanta ba.
An dai dauki tsawon shekaru 17 ana gudanar da harkokin kungiyar ba tare da an yi zabe ba, sai na riko.
Kamar yadda shugaban kwamitin shiryawa tare da gudanar da zaben, Alhaji Muhammadu Doro ya ce daga cikin mukamai 16 da ake da su, ofisoshi 4 ne aka gudanar da zaben a kansu, saura kuwa duk babu hamayya. Ofisoshin da abin ya shafa sun hada da na jami’i mai kula da shiyyar Funtuwa; Jami’in hulda da jama’a; Sakatare tare da na Shugaba.
Cikin tsarin da kwamitin ya yi don gudanar da zaben bisa ka’ida akwai tantance masu zabe, wato wakilai biyar daga kowace karamar hukuma; ba ’yan takara damar fadin ta bakinsu kafin zaben; sai kuma ba masu zabe damar zabar hanyar da suke gani ta fi dacewa, inda masu bukatar a yi zaben ’yar-tunke suka yi rinjaye.
Malam Ahmad Musa Mashi, daga shiyyar Daura shi ne ya yi nasara ak an abokin takararsa Malam Musa Amadu Funtuwa daga shiyyar ta Funtuwa, a kujerar shugabancin kungiyar. Sai Malam Garba Isa Tsauwa ya yi zarra a kan Malam Bishir Garba, a mukamin sakatare. Shi kuwa Malam danladi Ma’azu ya zama jami’in hulda da jama’a a kan Malam Abdussalamu Bawa. Kujerar jami’i mai kula da shiyyar Funtuwa ta fada wajen Malam Rabe danmalam, wanda ya rinjayi Malam Sule Musa. Malama Bilkisu Isa Gambarawa kuwa ita ce shugabar mata ba tare da hamayya ba.
A jawabinsa, bayan rantsuwar kama aiki, sabon shugaban ya ce za iyi iyakar kokarinsa na ganin kungiyarsu ta cigaba. “Allah Ya sani, muna bara ne ba don muna so ba, domin cikinmu har masu digiri akwai, ba difloma ba kadai, amma babu aikin yi, bayan kuma akwai wasu guraben da za mu iya cikewa. Ga sana’o’in hannu, irin su yin kujerun roba, darduma, takalma, jikka da sauransu, wadanda duk mun iya, to amma iyakarmu iyawar kawai. Ya kamata a ce, kamar yadda gwamnati ke sama mana wajen koyo, to ta biyo da tallafin inda za mu rika kai kayan da muka sana’anta don sayarwa, kamar yadda ake yi a wasu wuraren”.
Daga nan sai ya yi kira ga masu hannu da shuni da ke jihar ta Katsina da su rika tallafa musu domin samun jarin da za su rika dogaro da kansu da shi, maimakon bara.
Ita ma sabuwar shugabar mata, Malama Bilkisu Isa ta yi kira makamancin haka, inda ta yi nuni da cewa, ana bar musu marayu da ’yan mata, wadanda za su yi masu aure, amma rashin abin dogaro ke sa su yin barar. “Ina tabbatar maka hatta da kuli-kuli, mu mata makafi muna yi, kamar yadda masu ganin ke yi, amma saboda rashin jari babu yadda za mu yi, dole mu yi bara”.
Wani wakilin kungiyar na kasa, Mista Ezekiel, jami’i mai kula da shiyyar Arewa maso Yamma, yabawa ya yi da yadda aka gudanar da zaben, kuma ya yi fatar alheri kan haka, sannan ya yi kira ga ’ya’yan kungiyar kan hadin kai tare da taimaka wa harkokin cigaban kungiyar.
Mista Ezekiel ya bukaci gwamnati da sauran jama’a kan tallafa wa nakasassu. “Muna fita bara, har wani lokaci muna rasa ranmu, amma ba don muna so ba, sai don ya zamo dole. Muna da masu ilmi a cikinmu amma ba a kulawa a kan haka. Shin an jarraba mu an ga ba mu iya ba ne? Har kwamfuta mun iya, kuma cikinmu nan kadan ne ba su da wayar salula, shin muna ganin lambobin ko sunan wanda za mu kira ko ya kira mu? Ashe muna da wata baiwa da Allah Ya ba mu”, inji shi.
An dai yi zaben kungiyar lafiya, amma ba tare da halartar wakili, musamman daga ma’aikatar kula da nakasassu ba.