✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar Majma’u ta yi bikin mauludi a Abuja(2)

kungiyar Matasa Masu Yaki da Shaye-Shayen Miyagun kwayoyi  wato Youth Forum on Drugs Abuse da ke Kano (YAFODA) za ta fadada ayyukanta zuwa wasu jihohin…

kungiyar Matasa Masu Yaki da Shaye-Shayen Miyagun kwayoyi  wato Youth Forum on Drugs Abuse da ke Kano (YAFODA) za ta fadada ayyukanta zuwa wasu jihohin arewacin kasarnan domin ci gaba da aikin ilmantar da matasa illolin shan miyagun kwayoyi.
A jawabinsu daban-daban, Shugaban  kungiyar Malam Abubakar Mai Tumaki da Sakataren kungiya Malam Abdulrazak Ibrahim da kuma jami’in hulda da jama’a  na kungiyar Malam Isah Bello  sun bayyana cewa suna samun kyawawan nasarori wajen fadakar da matasa illolin shaye-shaye wanda  hakan ce ma ta sanya suka yanke shawarar fadada ayyukansu zuwa wasu jihohin arewacin kasar nan.
Har ila yau, shugaban ya ce kungiyar tana da alaka mai kyau tsakaninta da hukumomin tsaro da ke Jihar Kano tare da Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun kwayoyi (NDLEA).
A karshe  shugabannin kungiyar sun bayyana cewa  suna gudanar da gangami na wayar da kan  dalibai a makarantu da kuma tashoshin motoci, inda suka ce “muna jan hankalin al’umma muhimmancin barin shan miyagun kwayoyi ta yadda za a kawar da wannan  matsala  musamman ganin cewa lokaci ya yi da kowa zai zamo nagari cikin al’umma.”