✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar Majma’u ta yi bikin mauludi a Abuja

kungiyar Masoya Annabi mai suna Majma’u Ahbabun Nabiyyi (SAW) Wa Shaikh (RTA), ta gudanar da bikin mauludinta na shekara-shekara don nuna murnar zagayowar ranar da…

kungiyar Masoya Annabi mai suna Majma’u Ahbabun Nabiyyi (SAW) Wa Shaikh (RTA), ta gudanar da bikin mauludinta na shekara-shekara don nuna murnar zagayowar ranar da aka haifi Manzon Allah (SAW).
kungiyar ta yi bikin ne a babban Masallacin Juma’a na Sanusi dantata da ke Abuja a karshen makon jiya.
Alhaji Abubakar Isa Gula, ya bayyana cewa bikin mauludin da kungiyar ta gudanar shi ne karo na 17 da kungiyar ta shirya a kasa baki daya.
Ya ce kungiyar ta shirya taron ne don a tunatar da mutane girma da martaba Manzon Allah.
“Murna da haihuwar Annabi wanda ya kawo mana addinin Musulunci shi ne makasudin da ya sanya muka shirya taron mauludinmu na wannan shekara,” inji shi.
Da yake karin bayani, babban sakataren kungiyar, Malam Ibrahim Idris, ya bayyana cewa kungiyar na son cimma manufar hadin kan masoyan Annabi tare da gyara zuciyarsu.
Ya kara da cewa kungiyar tana son ta yi amfani da mauludin don fadakar da jama’a muhimmancin mauludi.
Ya yi kira ga daukacin Musulmi su yi watsi da tarzoma da kashe-kashe da ta’addanci da kuma gaba a tsakanin juna.
Daga nan ya yi kira ga Musulmi da Kirista su hada kai su zauna lafiya don alfanun kasa baki daya.
“Muna so mu yi amfani da wannan dama wajen kira ga daukacin ’yan Najeriya su hada kai su zauna lafiya da juna don ci gaban Najeriya,” inji shi.
Ya bayyana cewa kungiyar na fita da’awa don yada addinin Muslunci tare da tsarkake zuciyar wadanda suka karbi addini.
Sai dai kuma ya ce abin da ya bambanta su da sauran kungiyoyi shi ne sadaukar da kai.
A karshe ya ce: “Mu Shehunanmu sun nuna mana muhimmancin hidima. Saboda haka shi ya sa mu babu abin da muka sanya a gaba shi ne yi wa addini hidima ba tare da gajiyawa ba.”