✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta janye yajin aiki

Kungiyar Ma’aikatan Samar da Wutar Lantarki ta kasa (NUEE) ta janye yajin aikin da ta fara jiya Laraba. A jiya Laraba ne kungiyar ta NUEE…

Kungiyar Ma’aikatan Samar da Wutar Lantarki ta kasa (NUEE) ta janye yajin aikin da ta fara jiya Laraba.

A jiya Laraba ne kungiyar ta NUEE ta sanar da fara shiga yajin aikin ma’aikatan bayan sun bai wa Gwamnatin tarayya wa’adin kwana 21.

Jim kadan, bayan janyewar yajin aikin kungiyar ma’aikatan mahukuntan Kamfanin rarraba wutar lantarki ta jihar Kano KEDO ta sha alwashin inganta wutar lantarkin don bukatun jama’a musamman jihohin Kano, Jigawa da Katsina.

Kungiyar NUEE ta janye yajin aikin da ta fara ne bayan tattaunawar su da wakilan gwamnati da suka yi a safiyar yau, sun kuma tattauna dalilan sun a tsunduma cikin yajin aikin.