✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Ma’aikatan Jirgin Kasa ta Najeriya za ta yi zaben sabbin shugabanni

Kungiyar Ma’aikatan Hukumar Jiragen Kasa ta Najeriya (Nigeria Union of Railway Workers) ta bayyana kammala dukkanin shirye-shiryenta na gudanar da babban taro na kasa da…

Kungiyar Ma’aikatan Hukumar Jiragen Kasa ta Najeriya (Nigeria Union of Railway Workers) ta bayyana kammala dukkanin shirye-shiryenta na gudanar da babban taro na kasa da kuma gudanar da zaben sabbin shugabannin Kungiyar.

Taron, wanda za a gudanar a garin Kafanchan a ranar Alhamis mai zuwa, ana sa ran zai kunshi wakilai mutum 100 daga sassan kasar.

Yayin da yake yi wa Aminiya karin haske, shugaban riko na Kungiyar Mista Innocent Luka, ya ce dukkanin shirye-shirye sun kammala, kama masauki da tsaro da kuma gudanar da tsaftataccen zabe da kuma tabbatar da komai ya gudana cikin kwanciyar hankali.

Luka, wanda shi ma yake neman takarar shugabancin Kungiyar ya ce, za a gabatar da kasidu daban-daban kan abubuwan da suka shafi harkar sufurin jiragen kasa don duba yadda za a bunkasa harkar.

“Daga cikin abubuwan da zamu fi mayar da hankali a wajen taron shi ne zakulo hanyoyin da za a kyautatawa ma’aikata da dasa na’urori na zamani da samar da motoci ga dukkanin cibiyoyi bakwai da ke fadin Najeriya don saukaka hanyoyin tafiyar da aikace-aikacen kungiyar.

“Kamar yadda muke jinjinawa yunkurin gwamnatin Tarayya kan kokarin farfado da kuma inganta harkar sufurin jiragen kasa, har ila yau muna kira a gareta da ta sani harkar ba zai samu tagomashin da ya kamata ba ta hanyar gyara hanyoyi ba, tare da lura da jin dadin ma’aikatan da abin ya shafa ba.” In ji shi.

A karshe ya bayyana taron da za su yi da kuma zabubbukan da za su gudanar a matsayin hanyar cicciba harkar sufurin jiragen kasa zuwa mataki na gaba.