✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar M & B ta horar da mutane 4,000 sana’o’i

kungiyar M and B ta horar da kimanin mutane 4000 a fadin Jihar Kano sana’oi’ daban-daban don dogaro da kansu. Kwamared Muhammad Umar Barde shi…

kungiyar M and B ta horar da kimanin mutane 4000 a fadin Jihar Kano sana’oi’ daban-daban don dogaro da kansu. Kwamared Muhammad Umar Barde shi ne Shugaban kungiyar, ya bayyana wa Aminiya cewa sun kafa kungiyar ce kimanin shekaru da niyyar ganin al’ummar Jihar Knao musamman matasa sun sami sana’a. 

“Kishi da muke da shi na son ganin matasa sun dogara da kansu ya sa muka kafa wannan kungiya. Lokacin da muka gamsu cewa al’umarmu ta Jihar Kano tana neman dauki musamman matasanmu da zaman kashe wando ya yi wa katutu don haka muka zabura muka kafa  wannan kungiya don ganin mun ceto su daga wanann yanayi da suka shiga”  

kungiyar tana gudanar da ayyukanta a cikin makarantun sakandaren gwamnati a ranakun karshen mako. “Muna gudanar da ayyukanmu ta hanayar amfani da ajujuwan makarantun sakandare a cibiyoyi takwas da muke da su a cikin Jihar Kano. Dalilin da yasa muka rarraba abin har cibiyoyi takwas shi ne don sawkaka wa dalibanmu zirga-zirga. Idan ya kasance wasu suna Bachirawa to za su yi amfanin da cibiyarmu da ke Rijiyar Lemo ba sai sun taso sun je unguwar Dukawuya ba, haka ma wanda ke Gidan Zoo ba sai ya tafi Rimin Kebe ba. An yi hakan ne don saukaka wa al’umma.”

Kwamared Umar ya bayyana cewa suna gudanar da ayyukansu na horarwa kyauta ba tare da karbar ko sisin kwabo ba daga hannun wadanda ake horarwarwa.

A cewarsa don ganin sun sama wa kayayyakin da matasan ke sarrafawa kasuwa yanzu haka tuni suka yi rajista da kamfanin da ke yi wa kamfanoni na kasa rajista, don samun damar yin hakan ba tare da tangarda ba “Bincike ya nuna cewa yawancin masu sana’o’i na gida sukan sami kansu a matsalar rashin kasuwar kayayyakin da suke sarrafawa, hakan ya sa muka yi wa kungiyarmu rajista don samun damar shigar tare da tallata kayayyakin da ‘ya’yan kungiyar suke sarrafawa a ko’ina a fadin duniya.

Shugban ya yi kira ga gwamnati da ta tallafawa wadanda aka horar din da jarin da za su fara sana’a. Ita ma daya daga cikin mutanen da suka sami wannan horo mai suna Maryam Nasidi Ibrahim ta gode wa shugabannin kungiyar bisa wannan horo da suka yi musu.

A cewar Malama Maryam “”Za ki yi mamakin abubuwan da muka koya a cikin wata daya da mako guda da muka fara samun wanann horo. A yanzu na iya yadda ake yin jaka da takalmi da dinkin labule da shirin dutse na kwalliya da sauransu, babu abin da za mu ce da wanannan kungiya sai godiya.”