✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar Legas Unity da ta Fifth Chukker sun zama zakara a gasar kwallon dawaki ta Legas

kungiyar kwallon dawaki ta Lagas Unity ta lallasa takwararta ta Kano da ake kira Kano Tripple KKK da ci 6 da 3 inda hakan ya…

kungiyar kwallon dawaki ta Lagas Unity ta lallasa takwararta ta Kano da ake kira Kano Tripple KKK da ci 6 da 3 inda hakan ya sa kungiyar Lagas Unity ta zama zakara a gasar kwallon dawaki ta kofin Dansa.
Hakazalika kungiyar kwallon dawaki mai suna Lagas Fifth Chukker ta lallasa kungiyar Lagas Shoreline da ci 9 da 6 inda hakan ya sa ta zama zakara a gasar da aka gudanar a Legas a karshen makon da ya gabata.
Babu kungiyar da ta kai gaci a mintuna uku da fara gasar Kofin Dansa domin duk kokarin da dan wasa Glory Ebano ya yi na cin kwallo ya ci tura amma Abdulmuminu Musa ya raba gardama inda ya ci kwallo da bugun bayan hannu daga yadi 12 daga raga.
Daga nan sai Tata Ali Kura ya kara kaimi inda ya farke cin da aka yi musu. Amma duk kokarin da Hitman Kura da Farouk Ibrahim suka yi ya sanya Ebano ya ci kwallo wanda hakan ya sanya aka yi kunnen doki.
Daga bisani Musa Abdulmiminu ya ci kwallo inda hakan ya sanya kungiyar Lagas Unity ta zama a kan gaba da ci 2 da daya.
Musa wanda shi ne kyaftin din kungiyar kwallon dawaki ta Lagas Unity ya kara kaimi amma daga bisani Hakeem Shagaya ya ci kwallo daga tsakiyar fili a cikin dakika 30 wanda hakan ya ba Legas Unity ta zama a kan gaba.
Wasan ya kayatar  kuma ya ba ’yan kallo sha’awa musamman irin yadda ’yan kwallon suka rika nuna kwarewa da badaru daban-daban don su yi nasara a kan abokanen hamayyarsu.