✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Kwankwasiyya ta koya wa  mata 600 sana’o’i a Jihar Filato

Kungiyar Matasan Kwankwasiya ta Jihar Filato, ta yi yaye mata  600, da ta dauki nauyin koya musu sana’o’in hannu a garin Jos a ranar Lahadin…

Kungiyar Matasan Kwankwasiya ta Jihar Filato, ta yi yaye mata  600, da ta dauki nauyin koya musu sana’o’in hannu a garin Jos a ranar Lahadin da ta gabata.

An gudanar da bikin yayewar ce, a dakin taro na Babban Masallacin Juma’a na Jos.

Da yake jawabi a wajen, tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yaba wa kungiyar kan wannan kokari da ta yi, na daukar nauyin koya wa mata sana’o’i.

Ya ce wannan aiki yana daya daga cikin tsare-tsaren Kwankwasiya na taimaka wa al’umma.

“A tsarin Kwankwasiya a Jihar Kano, an dauki ’ya’yan talakawa  wadanda ba su san kowa ba, an biya musu kudaden karatu, sun tafi waje sun karanto fannoni da dama. Wannan shi ne muke bukata a taimaki marar shi ya tashi, shi ma ya taimaki wani,” inji shi.

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso wanda  Alhaji Bashir  Sanata ya wakilta, ya  ce idan ana taimaka wa matasa ana ba su ayyukan yi, ana koya musu sana’o’i kamar yadda wannan kungiya ta yi, za a magance matsalar tsaro a kasar nan.

Ya ce da yawa aure yana mutuwa, saboda maigida ya fita bai bayar da kudin cefane ba. Don haka idan aka tallafa wa mata aka koya musu sana’o’i suka dogara da kansu, za su rike gidajensu su bai wa yara tarbiyya. Kuma wata rana ko maigida bai bayar da kudin cefane ba, mace za ta iya yin wani abu.

A jawabin Shugaban Kungiyar Matasan Kwankwasiya ta Jihar Filato, Alhaji Sudais Salim ya ce sun shirya taron ne, domin su yaye mata 600 da suka dauki nauyin koya musu sana’o’in dinki  da kwalliya da girke-girke da man shafawa da man zafi da sauransu.

Ya ce sun tallafa wa mata ne domin su samu abin dogaro da kansu,  ganin cewa su ne  garkuwar al’umma da kuma  tausaya musu,  ganin kuncin rayuwar da ake ciki a kasar nan.

Har ila yau ya ce baya ga wannan, sun yi ayyukan kai ziyara gidajen yari  da gidajen marayu da asibitoci da makarantu inda su ma suka tallafa musu.

Ya  ce nan ba da dadewa  za su fara shirye-shiryen auren zawarawa a  jihar.  Ya ce saboda ganin ayyukan alherin da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso yake yi ne, ya sanya suka kafa wannan kungiya, don su yi koyi da shi.