✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar kwallon kafa ta Abia Warriors ta doke Anambra United

A gasar cin kofin ’yan kabilar Igbo da ke garin Kafanchan, kudancin Jihar Kaduna, kungiyar kwallon kafa ta Abia Warriors da ke garin Kafanchan ta…

A gasar cin kofin ’yan kabilar Igbo da ke garin Kafanchan, kudancin Jihar Kaduna, kungiyar kwallon kafa ta Abia Warriors da ke garin Kafanchan ta doke takwararta ta Anambra United a bugun daga kai sai mai tsaron gida (fanariti) bayan tashi canjaras da suka yi a wasan karshe na cin kofin ’yan kabilar ta Igbo karo na farko.

Wasan, wanda aka buga a sabon filin wasan kwallo na garin Kafanchan da ke Unguwar Musa, wanda kuma shugaban kungiyar al’ummar Igbo na garin Kafanchan Mista Martins Okoli ya jagoranta ya samu halartar mutane da dama. Shi dai wannan gasa wanda shi ne irinsa na farko a garin, ya kunshi zallan ’yan kabilar Igbo ne bisa la’akari da jihohinsu na asali ta yadda kowace kungiya ke amsa sunan ’yan asalin jihohin da suka fito.

Wasan, wanda aka fara shi karfe biyar da kwata saboda cece-kucen da ya faru kan batun saka wani dan wasa, dukkanin kungiyoyin sun yi ta kai wa juna hare-hare amma kowane mai tsaron gida ya gwada bajintarsa inda aka tashi babu kwallo a ragar kowa abin da ta kai ga bugun fanariti wanda ’yan wasan Anambra United suka zubar da kwallaye biyu su kuma Abia Warriors suka cinye nasu kwallayen.

An raba kyaututtuka ga wadanda suka yi nasara a gasar a jihohi daban-daban kuma shugabannin shirya gasar sun bayyana jin dadinsu tare da alwashin ci gaba da shirya irin wannan gasar lokaci bayan lokaci.