✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Kwadago ta kira zanga-zanga kan yajin aikin ASUU

NLC ta ce tunda tattaunawa ta ki samar da mafita, to za ta bullo wa gwamnati ta wata hanyar

Kungiyar Kwadago ta Najeriya ta umarci kungiyoyi fiye da 50 da ke karkashinta su fita zanga-zanga bisa yajin aikin da Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) ke yi na tsawon wata uku.

Kungiyar ta ce bayanan da ta samu na nuna babu wani cigaba da ake samu a tattaunawar Gwamnatin Tarayya da kungiyoyin jami’o’i na ASUU da SSANU da kuma NASU, har ma Kwalejojin Ilimi da na Fasaha.

A taron da suka gudanar ranar Alhamis, Shugaban NLC, Ayuba Wabba, ya ce matakin ya zamo dole duba da shakulatin-bangaro da gwamnati ta yi wa bukatun kungiyoyin manyan makarantun.

Don haka ya ce za su tabbatar gwamnati ta warware matsalolin kungiyoyin tunda tattaunawar gwamnatin da ASUU ba ta samar da mafita ba.

Wabba ya ce za a gudanar da zanga-zangar ce a fadin kasa baki daya da zummar jan hankalin gwamnati kan illar da yajin aikin ke haifarwa Najeriya da bangaren Ilimi  nan da sati guda.

Idan ba a manta ba dai kungiyoyin na yajin aikin ne tsawon watanni kan matsalolin biyansu ta tsarin IPPIS, da sauran bukatu da dama.