✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Kasashen Laraba za ta dawo da Syria cikinta bayan shekara 8 da korarta

Rahotanni daga majiyoyi da dama a bangaren harkokin diflomasiyyar kasashen Larabawa sun cewa Kungiyar Kasashen Laraba ta shirya domin dawo da kasar Syria cikinta shekara…

Rahotanni daga majiyoyi da dama a bangaren harkokin diflomasiyyar kasashen Larabawa sun cewa Kungiyar Kasashen Laraba ta shirya domin dawo da kasar Syria cikinta shekara 8 bayan cire ta, duk da cewa akwai turjiya daga wasu kasashen.

Jaridar The Guardian ta Ingila ta ruwaito cewa kasashe da dama daga cikin kasashe 22 na kungiyar sun nuna amincewarsu da batun bayan an tsagaita wuta a kasar.

An dai kiyasta cewa ana bukatar akalla Dalar Amurka biliyan 400 domin sake gina kasar, kuma Majalisar Dinkin Duniya ta ki sanya sisinta a ciki, har sai Assad ya jawo ta cikin ayyukan samar da zaman lafiya a kasar.

Hakan ya sa ake tunanin zai yi wuya a samu mukudan kudin da ake bukata, sai Saudiyya ta taimaka.

Shi kansa Shugaba Assad ya shaida wa wata jaridar Kuwait cewa kasarsa ta samu sulhu da yarjejeniya da wasu kasashen Larabawa. Kuma an gano Minsitar Harkokin Wajen Kasar, Walid Al Muallem yana gaisawa cikin raha da takwaransa na kasar Bahrain, Sheikh Khalid Bin Ahmed Al Khalifa a taron Majalisar Dinkin Duniya na karshe.

“Abin da ke faruwa a kasar Syria ya fi shafarmu sama da kowa a duniyar nan. Syria kasar Larabawa ce, don haka bai kamata lamuran kasar su koma wajen kasashen Yamma ba tare da sa hannunmu ba,” inji Khalifa.