✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar kabilun Kudancin Kaduna ta yi bikin al’ada a Jigawa

kungiyar SOKAPU wato kungiyar kabilun kudanchin Kaduna, ta yi bikin nuna ala’adu tare da kaddamar da kalandar kungiyar da nufin nema wa kungiyar kudin shiga…

kungiyar SOKAPU wato kungiyar kabilun kudanchin Kaduna, ta yi bikin nuna ala’adu tare da kaddamar da kalandar kungiyar da nufin nema wa kungiyar kudin shiga a Dutse.

A yayin bikin baje al’adun, ‘ya’yan kungiyar wadanda suka hada da Gwari da Kataf da sauran kabilu, an gabatar da al’adu da raye-raye iri-iri, kuma an tara wa kungiyar kudi sama da Naira dubu dari biyu a lokacin da aka sayar da kalandar kungiyar. 

Gudunmawa mafi tsoka ta fitone daga wajen babban mai kaddamarwa, Mista Danjuma Ibrahim wanda ya sayi kalanda guda daya akan naira N30,000. Sai masarautar Dutse, wanda dan isan Dutse, Alhaji Jazuli Nuhu ya wakilta ta sayi guda biyu a kan kudi naira 20,000, sai Hadiza Chiroma da saya guda daya a kan naira N10,000 da madam Kubuli danmaraya ta sayi daya a kan naira N10,000

Da yake jawabinsa na bude taro, shugaban kungiyar SOKAPU Mista Bala Musa ya ce kungiyar kungiya ce da ta hada kabilu daban dabam da suka hadu.  Kuma an kafa ta ne da nufin taimakon juna a Jihar jigawa da kulla dankon zumunci da sauran mutane a fadin Najeriya.

Da ya juya kan irin ayyukan cigaba da kungiyar ta samar da kuma irin alakarsu da masarautar Dutse, ya ce masarautar Dutse ta taimakawa kungiyar ta fannoni da dama, ta kuma tabbatar da nadin daya daga cikinsu a matsayin sarkin SOKAPU a nan Jihar ta Jigawa, wanda ta bakinsa ne duk wani sako da yake fitowa daga masarauta ‘yan kungiyar suke sani, haka fadar Gwamnatin Jihar idan akwai sako ta wajansa ne suke ji. 

Ya kara da cewa daya daga cikin abin alfaharinsu da ba za su manta ba shi ne filin da Gwamnatin Jihar ta ba su tare da taimakon fadar Dutse, inda ya ce suna godiya. 

Sai kuma ya nuna damuwarsa game da rashin kudi da kungiyar take fuskanta wanda shi ne ya yi wa kungiyar dabaibayi wajen gina ofishin na ta afilin da Gwamnatin Jihar ta mallakamata. Saboda ne shugaban kungiyar ya bukaci ‘ya’yan kungiyar na ciki da wajen jihar da su tallafa.