✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Izala ta tura masu tafsiri 533 a ciki da wajen Najeriya

Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa, ta tura malamai masu tafsiri 533 zuwa garuruwan daban-daban na Najeriya da kasashen waje. Shugaban Majalisar…

Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa, ta tura malamai masu tafsiri 533 zuwa garuruwan daban-daban na Najeriya da kasashen waje.

Shugaban Majalisar Malamai ta Kasa ta Kungiyar, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ne ya bayyana haka lokacin da yake bude tafsirin azumin watan Radaman da yake gabatarwa a garin Jos.

Ya ce ya kamata kowa ya yi karatu, domin idan kowa ya yi karatu al’umma za ta yi karfi. Kuma za a samu kwanciyar hankali da natsuwa. “Don haka kungiyar take tura malamai masu tafsiri lokacin azumin watan Radaman zuwa wurare daban-daban,” inji shi.

Ya ce “Ba za a iya yin Musulunci ba, idan babu ilimi kuma ba za a samu ilimi ba, idan babu karantarwa. Don haka mu tausaya wa ’ya’yanmu da matanmu wajen karantar da su addinin Musulunci, domin nan ne alherin duniya da Lahira yake.”

Ya yi kira ga ’yan kasuwa su rage farashin kayayyakin da suke sayarwa a wannan wata na Ramadan. Ya ce duk dan kasuwar da ya rage farashin kayansa, lokacin watan azumi zai samu lada mai yawa.

Har ila yau, ya yi kira ga masu hannu da shuni su tallafa wa marasa galihu musamman wajen ciyarwa da tufatarwa a wannan wata.

Sheikh Jingir ya yi kira ga gwamnatin Buhari ta kyautata wa talakawan Najeriya,  ta hanyar cika alkawuran da ta yi musu.  “Talakawan Najeriya Allah Ya sa musu son Buhari saboda gaskiyarsa, don haka suka sake fitowa suka zabe shi, a karo na biyu. Babu irin wahalar da talakan Najeriya bai sha ba kan zaben Buhari. Don haka gwamnatin Buhari ta tallafa wa talakan Najeriya,” inji shi.