Kungiyar Jama’atu Izalatul Bidiah wa Iqamatis Sunnah reshen Jihar Neja ta kaddamar da asusun samar da cibiyar koyon sana’o’i, da kuma kammala ginin makarantun firamare da sakandaren Minna.
Kungiyar ta kuma ce cikin kudin da ya kai N306,600,000 ,000, za ta gina sakatariyarta, da sayen motar kai marasa lafiya asibiti, hadi da bas-bas da za su dinga gudanar da ayyaukansu.
- A haramta wa Iran shiga Gasar Kofin Duniya —Ukraine
- Ilimin yara mata: Kaduna ta tura malamai 2,000 zuwa makarantu 155
Babban sakataren tsare-tsaren kungiyar, Dokta Mas’ud Ibrahim Tulu ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Minna, babban birnin jihar.
Ya bayyana cewa hakan ba karamin tallafa wa gwanamti zai yi ba, domin za su horas da matasan ne sanao’i daban-daban, don su dogara da kawunansu.
Da yake jawabi yayin taron, Shugaban Majalisar Malamai na shalkawatar kungiyar Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ya ce cibiyar ta zo a lokacin da aka fi bukatarta, sakamakon fama da kuncin rayuwa da al’umma ke yi.
Sheikh Jingir ya yi kira ga sarakunan yankin hadi da ma’aikatan gwamnatin Jihar da su zamo ababen misali ga al’ummar, domin guzurin alkiyamarsu.