✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar Izala ta bude babban asibiti a Jos

A ranar Lahadin da ta gabata ne kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa ta bude babban asibitin da ta gina kan kudi fiye…

A ranar Lahadin da ta gabata ne kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa ta bude babban asibitin da ta gina kan kudi fiye da naira miliyan 100.
Asibitin mai gadaje 60, wanda aka rada wa sunan, Sunnah Hospital Jos, yana a Unguwar Rimi da ke garin Jos babban birnin Jihar Filato.
Da yake jawabi a wajen bikin gwamnan Jihar Zamfara Alhaji  Abdul’aziz Yari Abubakar, ya yaba wa kungiyar kan  gina asibitin. Ya ce: “Aikin gina asibiti da kungiyar ta yi wani babban ci gaba ne ga al’ummar Musulmin kasar nan.”
Gwamnan wanda sakataren gwamnatin Jihar Farfesa Abdullahi Muhammad Shinkafi  ya wakilta ya yi kira ga sauran kungiyoyin addinin Musulunci da ke kasar nan,  su yi koyi da wannan aiki da kungiyar  ta yi, ta hanyar karkafa gina irin wadannan asibitoci.
Shi ma a nasa jawabin gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong ya bayyana cewa babu shakka wannan asibiti zai taimaka wa al’umma baki daya, wajen kula da lafiya. Don haka ya ce gwamnatin jihar ta yi matukar farin ciki da gina sa.
Gwamnan wanda mataimakin shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar, Barista Yusuf Gambo Hawaja ya wakilta ya yi bayanin cewa a kullum a shirye gwamnatin jihar take wajen ganin ta hada hannu da irin wadannan kungiyoyi don ganin an ciyar da jihar gaba.
A nasa jawabin shugaban majalisar malamai na kungiyar na kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya bayyana cewa kiwon lafiya yana daga cikin ayyukan da addinin Musulunci ya yi umarnin a kula da su.