Mutum 32 maza da mata ne suka amfana da shirin aurar da marasa karfi da Kungiyar Mata Musulmi ta Kasa (FOMWAN) reshen Jihar Kano da hadin gwiwar wata kungiya daga kasar Turkiyya mai suna Daru Arkam Charity Foundation suka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata.
Da take jawabi a kan makasudin yin auren, Shugabar Kungiyar FOMWAN Malama Fatima Abubakar Umar ta ce “Mun lura cewa da yawa mutane suna son yin aure, amma hakan ya gagara saboda matsin tattalin arziki da ake ciki. Shi ya sa muka dauki wannan bangare don magance wannan matsala.”
- Sana’ar fawa a Kudu tamkar jihadi ne —Sarkin Fawa
- Gobara a tashar nukiliya; fararen hula na barin biranen da Rasha ta kwace
Game da yadda aka zabo ma’auratan, Malam Fatima ta ce sun dauko mutane daga kowane bangare na kananan hukumomin jihar 44.
“Bayan mun zabo wadanan ma’aurata wadanda dama tun farko suna son junasu suna shirin aure, amma wasu dalilai sun hana sai muka tantance matsayin lafiyarsu da gudanar da bincike game da sana’ar da angwayen ke yi don samun dorewar zaman auren”, inji ta.
Ta kara da cewa, “Ina yi wa wadanda ba su shiga cikin wannan shiri a yanzu ba albishir cewa nan ba da dadewa ba za a sake gudanar da makamancin wannan aure wanda muke fata mu ci gaba da yi koyaushe don ganin an kawar da matsalar rashin aure a tsakanin al’ummarmu.”
Ta ce sun tanadar wa ma’auratan kayan lefe da kudin sadaki da kayan abinci da ma’arautan za su ci na tsawon wata shida.
A jawabin Kwamishinar Harkokin Mata ta Jihar Kano Dokta Zahra’u Muhammad Umar ta ce tuni shirye-shirye suka yi nisa na sake gudanar da auren zawarawa da ’yan mata a jihar.
Kwamishinar ta nanata kudirin Gwamnatin Jihar Kano na shirya irin wannan aure, inda ta bayyana kalubalen tattalin arziki tun daga lokacin COVID-19 a matsayin daya daga cikin manyan kalubalen da suka jinkirta shirin.
Dokta Zahra’u Umar ta ce, da yardar Allah shirin zai gudana ne ta hanyar Ma’aikatar Mata don haka za ta fi ba wa marayu da marasa galihu muhimmanci.
Sai ta bukaci ma’auratan da su yi biyayya ga juna, kuma su bi ka’idojin aure kamar yadda suke a Musulunci.
Ta yaba wa kokarin Kungiyar FOMWAN da DARUL ARKAM da suka shirya auren tare da yin kira ga kungiyoyi masu zaman kansu su yi koyi da wannan kyakkyawan aiki.
Ma’auratan da suka ci gajiyar shirin sun gode wa wadanda suka shirya, inda suka sha alwashin rike junansu da amana.
Malama Fatima Abubakar wacce ta fito daga garin Walawa a Karamar Hukumar Dawakin Tofa amarya ce da ta amfana da shirin ta ce za ta yi biyayyar aure ga mijinta kuma ta gode wa wadanda suka yi musu wannan tagomashi.
Wani ango mai suna Malam Auwal Ali Tsanyawa ya bayyana farin cikinsa, wanda ya ce farin cikinsa ba zai misaltu ba, inda ya yi alkawarin zaman lafiya da matarsa har karshen rayuwarsu.