kungiyar Fityanul Islam ta kasa ta yi bikin cika shekara 50 da kafuwa a Gidan Arewa da ke Kaduna a ranar Lahadin da ta gabata, inda ta karrama shehunnai da dama.
An fara bukukuwan ne a ranar Juma’ar da wa’azi a masallacin Sheikh dahiru Bauchi da keTudun Wada, inda Sheikh Arabi da Sheikh Sani Khalifa da Sheikh Abdulkadir Zariya da kuma Sheikh Mai Nasara Liman suka gabatar da wa’azin.
Washegari Asabar kungi-yar ta gudanar da taron na Gidan Arewa mai taken: ‘Tarbiyyar Musulunci ita ce tushen ci gaban kowace Al’umma,’ inda Sheikh Ibrahim Makari Zariya da Sheikh Bashir Tijjani Usman suka gabatar da jawabai. A ranar Lahadi bayan da Sheikh dahiru Bauchi ya yi jawabi an mika lambobin yabo ga gwamnonin jihohin Kaduna da Kano da Neja da Nassarawa da Jigawa da Legas da Gombe da Borno da kuma Kwara.
Cikin shehunnai da aka karrama akwai Sheikh Ibrahim Inyass da shugaba da sakataren kungiyar na farko, Sheikh Abubakar Atiku Sanka da Sheikh Tijjani Usman da Sheikh dahiru Usman Bauchi da Khalifa Isyaka Rabi’u da Sheikh Mahmud Salga da Sheikh Zubairu kasim da sauran shehunnai.
Kuma an kafa gidauniya don aikin gidan marayu na kungiyar a garin dan Kande, inda gwamnatin Jihar Kaduna ta ba da Naira miliyan 10, sai Borno da Neja da Mataimakin Shugaban kasa Namadi Sambo, Naira miliyan biyar-biyar.
Gwamnatin Katsina Naira miliyan 2, Kwara Naira miliyan 1, Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura Naira Dubu 500, yayin da Sanata Abu Ibrahim ya ce zai gina wa kungiyar cibiyar ilimin kwamfuta a Jihar Katsina don taimakawa wajen inganta ilimin zamani.
kungiyar Fityanul Islam ta yi bikin cika shekara 50
kungiyar Fityanul Islam ta kasa ta yi bikin cika shekara 50 da kafuwa a Gidan Arewa da ke Kaduna a ranar Lahadin da ta gabata,…
