✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Fasahar Kwaikwayo za ta shirya wa marayu wasan kwallon kafa a Bauchi

A kokarin da suke yi na sanya walwala da kyautata jin dadin yara marayu da marasa galihu, kungiyar Fasahar Kwaikwayo mai shirya finafinan Hausa mai…

A kokarin da suke yi na sanya walwala da kyautata jin dadin yara marayu da marasa galihu, kungiyar Fasahar Kwaikwayo mai shirya finafinan Hausa mai Suna Ganuwa Film Production ta bayyana aniyarta na shirya wasan kwallon kafa ga marayu da marasa galihu a Jihar Bauchi.

Shugaban kungiyar Alhaji Bala Hussaini DDK ne ya bayana haka a lokacin da suka kai ziyara gidan marayu na Jihar Bauchi domin ba su tallafi a ci gaba da ayyukan taimakon alu’mma da suke yi a Jihar Bauchi.

Alhaji Bala ya ce manufar bada tallafin shi ne domin ‘yan wasan kwaikwayon su yi mu’amala da su marayun da nufin kara martabarsu da darajarsu a cikin alu’mma,

Ya ce wannan ziyara zai sa marayun su ji cewa suma ‘ya’yane kuma al’umma ta damu da su kuma za ta kula da su sannan sun yi musu wasan kwaikwayo wanda zai kayatar da marayun ya sanya su cikin farin ciki da annashuwa.

Sai ya bada tabbacin cewa za su rika zuwa lokaci zuwa lokaci suna yi musu wasan kwaikwayo don kara sanya su cikin nishadi kuma hakan zai bai wa masu basira cikinsu damar yin amfani da basirarsu idan sun girma domin cigaban kasa.

Alhaji Bala ya ce su ne za su samar da dukan kayayyakin da za a bukata don yin wasan kuma suna sa ran al’ummar Jihar Bauchi za su goyi bayan wasan wanda suke sa ran Uwargidan Gwamnan Jihar Bauchi Hajiya Hadiza Mohammed Abubakar za ta halarta.