✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Falconets ta sauka garin Binin don karawa da Tanzaniya

Kungiyar kwallon  kafa ta mata zalla ta ’yan kasa da shekaru 20 mai suna Falconets ta isa garin Binin da ke jihar Edo don karawa da…

Kungiyar kwallon  kafa ta mata zalla ta ’yan kasa da shekaru 20 mai suna Falconets ta isa garin Binin da ke jihar Edo don karawa da takwararta ta kasar Tanzaniya a ranar Asabar mai zuwa.
Kungiyoyin biyu za su taka leda a kokarinsu na samun tikitin shiga gasar kwalon kafa ta mata da duniya ta shekarar 2018.
Wata sanarwa da hukumar kwallon kafa ta kasa ta fitar a yau ta nuna cewa mai horar da ’yan wasan kungiyar, Chris Danjuma shi ya jagoranci ’yan wasan tare da manyan hukumar daga Abuja zuwa birnin Binin.
Sanarwar ta nuna Danjuma ya dade yana horar da ’yan matan na tsawon makonni uku a garin Abuja kuma yana fatan ’yan matan za su yi nasara. Akan abokan hamaiyyarsu na kasar Tanzaniya.