✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Dattawan Arewa ta bukaci Majalisa ta tsige Buhari

Muddin Buhari ya gaza, babu dalilin da zai sa Majalisa ba za ta dauki mataki a kansa ba.

Kungiyar Dattawan Arewa ta Nothern Elders Forum (NEF), ta bukaci Majalisar Dokokin Tarayya da ta tsige Shugaba Muhammadu saboda ci gaba da tabarbarewar tsaro a kasar.

Mai Magana da yawun kungiyar, Dokta Hakeem Baba Ahmed, ya ce ba zai yiwu a a zuba ido Najeriya ta shiga wani mummunan yanayin da ba zai yi wa kowa dadi ba a yayin da Buhari ya gaza sauke nauyin da rataya a kansa na tsare lafiya da dukiyoyin al’umma.

A hirarsa da sashen Hausa na BBC, Baba Ahmed ya ce, duba da yadda ’yan kasar ke ci gaba da kokawa kan matsalolin da kasar ke fuskanta, Shugaba Buhari yana da zabin ya sauka kasancewar ya gaza ko kuma majalisar ta tsige shi.

Ya ce ’yan Majalisun Tarayya na da hurumin nazarin halin da kasa ke ciki da kuma duba a kan abinda gwamnati ta ce tana yi da kuma tanade-tanaden da kundin tsarin mulki ya yi domin daukar mataki a kai.

“Muddin Buhari ya gaza sauke nauyin da rataya a wuyansa, babu dalilin da zai sa Majalisa ba za ta dauki mataki a kansa ba.

“Abin takaici Najeriya ba ta da Majalisar da ke da kishin kasa da kuma halin da kuma rashin nuna damuwa kan halin da ake ciki, sai dai goyon bayan jam’iyyar da ’ya’yanta suka fito.

“Baba Ahmed ya ce a halin yanzu Najeriya na matukar neman shugabanci saboda haka ana bukatar aiki a zahiri maimakon surutu da yi wa jama’a alkawuran da ba a cikawa.

“Da a ce da gaske gwamnatin nan tana daukar matakai da tuni ta kai China ko da a ce tattakawa take yi,” a cewar Tsohon Sakataren Gwamnatin Kasar.

Aminiya ta ruwaito cewa, a Talatar da ta gabata ce Shugaba Buhari ya jagoranci taron Majalisar Tsaro a Fadar Gwamnatin Najeriya da ke Abuja, babban birnin kasar.

Wannan taro shi ne makamancinsa karo na uku cikin mako biyu da shugaban kasar ya jagoranta, inda ake tattauna batutuwan da shimfida tsare-tsaren da za su kawo karshen matsalar tsaron da ta dabaibaye kasar.