Kungiyar Daliban Najeriya Shiyyar C, ta karrama Shugaban Makarantar Kiwon Lafiya ta Sahlan da ke Jos a Jihar Filato, Malam Muhammad Shafi’u Yakub, kan gudunmawar da yake bayarwa wajen bunkasa ilimi.
Da yake jawabi a lokacin da yake mika masa shaidar karramawar, Shugaban Kungiyar, Gyang Moses Shut, ya ce aikin kungiyar ce ta duba tare da gano mutanen da suka bada gudunmawa a fannonin bunkasa ilimi da tattalin arziki da siyasa da masana’antu da samar da ayyukan yi, domin ta karrama su da zimmar karfafa musu gwiwa.
Ya ce a binciken da suke yi ne suka gano wannan matashi kuma Shugaban Makarantar Kiwon Lafiya ta Sahlan, kan irin gudunmawar da yake bayarwa, wajen bunkasa ilimi da tattalin arziki ta hanyar makarantar da ya bude.
Ya ce hakan ne ya sa suka karrama shi da nufin karfafa masa gwiwa kan wannan aiki da ya sanya a gaba.
Ya ce kungiyar tana alfahari da shi, don haka za ta ci gaba da goya masa baya, kan wannan aiki da ya sanya a gaba.
Da yake mayar da jawabi, Malam Muhammad Shafi’u Yakub, ya bayyana matukar farin cikinsa da wannan karramawa da kungiyar daliban ta yi masa.
“Ban san cewa wannan kungiya ta san ni ba. Sai ga shi sun bugo mini waya daga ofishinsu suka bayyana cewa sun duba sun ga wasu abubuwa na ci gaba da na yi wa al’umma, don haka suka ga ya dace su karrama ni,” inji shi.
Ya ce karramawar da aka yi masa za ta dada karfafa masa gwiwa, wajen ci gaba da abubuwan da yake yi na kawo ci gaba ga al’umma.