✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar dalibai ta Hayin Banki za ta shirya bita kan zaman lafiya

Kungiyar dalibai ta Hayin Banki da ke karamar Hukumar Kaduna ta Arewa a Jihar Kaduna (HABSU) za ta shirya taron bita na musamman a kan…

Kungiyar dalibai ta Hayin Banki da ke karamar Hukumar Kaduna ta Arewa a Jihar Kaduna (HABSU) za ta shirya taron bita na musamman a kan zaman lafiya da mutunta juna.

Shugaban Kwamitin amintattu na kungiyar, Malam Abdullahi Idris ne ya sanar da hakan a lokacin da yake zantawa da wakilin Aminiya a kan shirye-shiryen kungiyar.

A cewarsa, wannan taron na bita zai kunshi iyayen gari, jami’an tsaro na gwamnati da ‘yan bangan Unguwar da ake kira Jarumai Da Gora da sauran masu ruwa da tsaki a harkar tabbatar da zaman lafiya.

“Makasudin shirya wannan bita shi ne muna so mu tara dukan iyayen wannan gari na Hayin Baki Kaduna da jami’an tsaro na gwamnati da kuma Jarumai Da Gora wadanda su ne suke kokari domin Unguwar Hayin Banki ta zauna lafiya.

“kasancewar wadannan mutane kullum suna hana idonsu barci domin kare mutane. Shi ya sa muka ce bari mu bayar da gudunmuwa ta hanyar shirya musu bita a kan yadda za su rika tafiyar da lamuransu,” inji shi.

Da ya juya kan asalin makasudin assasa wannan kungiyar ta dalibai, Malam Abdullahi cewa ya yi sun kafa wannan kungiya ne da nufin taimakon ‘yan Unguwar musamman dalibai da suke karatu a manyan makarantu da kuma wadanda suke shirin shiga makarantun. “Mun bude wannan kungiya ce domin taimakon yaranmu masu karatu. Mukan koyar da su, mu ba su shawara a kan yadda za su yi karatu, da kuma shawara a kan fannin da ya kamata su karanta bayan mun lura da yanayin fahimtarsu. Sannan kuma muna da shiri na musamman da muke yi domin koyar da matasa sana’o’in da za su yi dogaro da kansu, da kuma koyar da sana’o’i sannan kuma idan hali ya yi mu ba su jari. Sannan kuma muna da bangaren yaki da jahilci. A takaice dai muna kwamitoci guda hudu: Kwamitin ilimi, da koyar da sana’o’i, da na wayar da kan al’umma, da na kiwon lafiya.

“kuma da muka lura cewa karatu ko koyar da shi bai yiwuwa sai da zaman lafiya. Sai muka ce bari mu shiga harkar samar da zaman lafiya domin mu bayar da gudunmuwa. Amfani masu ilimi shi ne su amfanar da al’umma ta kowane bangare.”

Hakanan kuma malam Abdullahi ya yi godiya ta musamman ga sarakunan Hayin Banki, Malam Mahmud Shehu Galadima da kawaransa na Unguwar Jauro Malam Bilyaminu Galadima bisa yadda suke ba kungiyar hadin kai da goyon baya.