✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kungiyar Ci gaban Masarautar Doma ta karrama Gwamnan Gombe

Muna alfahari da dan mu mai kishi wanda ba a samu kamarsa.

Kungiyar Ci gaban Masarautar Doma da aka fi saninta da Jekadafari a Jihar Gombe, ta karrama Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya da lambar yabo.

Da yake jawabi a yayin taron bayar da lambar yabo, Shugaban Kungiyar ta Jekadafari Forum, Bashir Nuhu Aliko cewa ya yi kungiyar ta yi la’akari da cancantar Gwamnan wajen bashi wannan lambar yabo kari a kan kasancewarsa dan Jekadafari.

Bashir Aliko, ya ce gwamnan ya yi abun ban mamaki musamman yadda ya cire wa al’ummar Gombe kitse a wuta ta hanyar samar da ayyukan madalla bila adadin a fadin jihar cikin tsawon shekaru biyu da suka gabata.

“Muna alfahari da dan mu mai kishi wanda ba a samu kamarsa, wanda hakan ya sa muka hada kai a kungiyance muka bashi lambar yabo,” inji shi.

Da yake nasa jawabin, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana godiyarsa ga kungiyar ta Jekadafari Community Forum bisa wannan karamci da ta nuna masa.

Gwamnan ya kara mika godiyarsa ga kungiyar kan aniyar da ta kudirta domin dawo da hadin kai da kaunar juna a tsakanin al’ummar Doma musamman ta hanyar samar da tallafi ga mabukata.

A nasa tsokacin, Shugaban Kungiyar Dokta Lawan Bala, ya ce sun shirya wannan taron ne a bainar jama’a domin nuna wa duniya cewa dansu ya taka rawar gani.

Shi kuwa Hakimin Doma Alhaji Abdullahi Maikano, ya ce rawar gani da Gwamnan ya yi a shekaru biyu na mulkinsa ce ta sanya Majalisar  Masarautar Doma ta nada shi a matsayin Santurakin Doma.

Ya kara da cewa, a baya can Hakimai na matakin albashi na shida tun bayan kirkiro Masarautar shekara 17 da suka gabata, inda a yanzu Gwamnan ya mayar da su matakin albashi na 12 wanda hakan abun a yaba ne.

Aminiya ta ruwaito cewa, a karshen taron ne ake tallafa wa matasa 500 masu aiki a rumfunan zabe da kudi naira dubu goma-goma.