kungiyar Kiristoci ta CAN reshen Jihar Neja ta zabi sababbin shugabannin kungiyar wadanda za su jagoranci Kiristocin jihar don kai su tudun-mun-tsira.
Zaben wanda aka gudanar a hedikwatar kungiyar da ke cikin birnin Minna a karshen makon da ya gabata, an yi shi lami lafiya, ba tare da wata hatsaniya ba a tsakanin ’yan takarar.
An zabi Rabaran Mathias Echioda a matsayin shugaba sai Rabaran FR. Godwin Yari a matsayin mataimakin shugaba sai Banerabil Silas Yisa a matsayin sakataren kungiyar da kuma sauran shugabannin da aka zaba a mukamai daban-daban.
Da yake jawabi jim kadan bayan bayyana sakamakon zaben, sabon shugaban kungiyar ta CAN Rabaran Mathias Echioda ya yi alkawarin yin aiki tukuru domin daukaka martabar kungiyar.
Ya ba mambobin kungiyar tabbacin cewa majami’u a jihar za su kasance wuraren addu’a a maimakon yadda wasu suka mayar da su dandanlin siyasa a baya.
Daga nan ya yi alkawarin cewa zai tabbatar da ganin kungiyar ta zama tsintsiya madaurinki daya tare da kare maradun Kiristocin jihar a kodayaushe.
Da yake jawabi bayan kammala zaben, Shugaban kungiyar Kiristoci ta CAN na jihohi 19 da ke Arewacin Najeriya, Rabaren Dokta Yakubu Pam, ya bukaci sabon shugaban kungiyar ta CAN ya tsaya kan gaskiya.
Rabaren Pam ya umarce shi da ya jajirce don ganin ya kawar da siyasa a majami’u da ke daukacin Jihar Neja.
Ya yi kira ga daukacin Kiristocin jihar su bai wa sabon shugaban goyon baya don a ganinsa shugaban zai iya kai kungiyar ga gaci har ta cimma burin da ta sa a gaba.
kungiyar CAN ta zabi sabbin shugabanni a Neja
kungiyar Kiristoci ta CAN reshen Jihar Neja ta zabi sababbin shugabannin kungiyar wadanda za su jagoranci Kiristocin jihar don kai su tudun-mun-tsira.Zaben wanda aka gudanar…