✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Boko Haram ta fara karban haraji

  Kungiyar Boko Haram ta fara karban haraji a hannun mutane a jihohin Borno da Yobe da wasu sassa a yankin Tafkin Chadi kamar yadda…

 

Kungiyar Boko Haram ta fara karban haraji a hannun mutane a jihohin Borno da Yobe da wasu sassa a yankin Tafkin Chadi kamar yadda Premium Times ta ruwaito daga Reuters.

Kamfanin Dillancin Labaran na Reuters ya ruwaito cewa bangaren na Boko Haram mai biyayya ga IS yanzu haka tana rike da kasa mai fadin kimanin kilomita 160 a jihohin Borno da Yobe, inda suka fi fama da rikicin na Boko Haram.

Harajin da suka xorawa mutane ya hada da makiyaya da suke biyan kimanin Naira 2,500 ga kowane shanu sai kuma Naira 1,500 a kan kananan dabbobi.

Hakanan kuma ‘yan Boko Haram din suna mayanka, inda suke yankawa mutane dabbobi suna karban sashin dabbab da suka yanka a matsayin lada.

“Idan kai makiyayi ne ko direba ko mai shago, ba za su taba ka, kawai ka bi umarninsu da dokokinsu,” kamar yadda wani makiyayi da ya so a ambaci sunansa ya sanar da Reuters. Sannan ya kara da cewa ba sa taba fararen kaya, jami’an tsaro kawai suke tabawa.”  

Hedkwatar Tsaro ba ta karyata rahoton ba kai tsaye, amma ta karyata batun cewa Boko Haram suna rike da wani bangaren kasa a yanzu haka.

“ Suna sanya mutane cikin matsi ne a duk lokacin da suka kama su. Bana tunanin wannan sabon abu ne, inji mai magana da yawon hedkiwatar tsaron Najeriya John Agim a lokacin da yake zantawa da Premium Times, sannan ya kara da cewa, “Boko Haram sun dade suna sanya mutane cikin wahala, amma wannan ba ya nufin cewa suna rike da sassan jihohin.”

“Amma muna aiki tukuru a game da lamarin domin magance matsalar.”