✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar ASUU ta kauracewa Gwamnatin Tarayya

Kungiyar Malaman Jami’a ta ASUU ba ta halarci taron da Gwamnatin Tarayya ta kira kan yajin aikin da membobin kungiyar suke yi. Sanata Chris Ngige,…

Kungiyar Malaman Jami’a ta ASUU ba ta halarci taron da Gwamnatin Tarayya ta kira kan yajin aikin da membobin kungiyar suke yi.
Sanata Chris Ngige, Ministan Kwadago da Ayyuka ya nemi shugabannin kungiyar ASUU da Ministan Ilimi da sauran masu ruwa da tsaki taro a Abuja dangane da kokarin da gwamnati ke yi na kawo karshen yajin aikin da kungiyar take yi.
Membobin kungiyar sun shiga yajin aikin sai-baba-ta-gani a ranar 13 ga watan Agusta bayan da Gwamnatin Tarayya ta kasa cika yarjejeniyar da kungiyar ta cimma da gwamnatin tarayya a watan Nuwamban shekarar 2016.