✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kungiyar ASUU ta janye yajin aiki

Shugaban ASUU, Biodun Ogunyemi ya sanar da hakan a safiyar Laraba

Shugaban Kungiyar Malaman Jami’a ta Najeriya (ASUU) Biodun Ogunyemi ya ce kungiyar ta janye yajin aikin da ta shafe kusan wata 10 tana yi.

Ogunyemi ya sanar da hakan ne a safiyar Laraba a Abuja, bayan taron Kwamitin Zartarwar Kungiyar a Abuja.

Sai dai ya ce akwai sharadi da kungiayr ta sanya a janye aikin da ta yi.

Sanarwar na zuwa ne bayan ASUU da Gwanatin Tarayya sun daidaita kan muhimman batutuwan da suka sa malaman shiga yajin aiki na twason wata 10.

Bayan tatataunawar Bangarorin biyu sun cimma matsayar kan yajin aikin malaman jami’ar, inda suka daidaita kafin wayewar garin Laraba.