kungiyar Apurima Onlus tare da hadin gwiwar hukumar bunkasa kasashe ta Majalisar dinkin Duniya (UNDP) ta koya wa matasa 149 sana’o’i da suka hada dinki da gyaran takalma da gyaran gashi da dafa abinci da sarrafa kwamfuta tare da raba masu kayayyakin wadannan sana’o’i a garin Bukur da ke karamar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato a ranar Asabar.
A jawabinsa a wajen raba kayayyakin shugaban kungiyar Mista Godwin Okoko ya bayyana cewa sun yi wata 6 suna koya wa matasan wadannan sana’o’in.
Ya ce a lokacin da suke koyar da matasan sun rika ba kowane mutum Naira dubu 15 a duk wata.
“Bayan da muka kammala koya musu wadannan sana’o’i, hukumar bunkasa kasashe ta majalisar dinkin duniya (UNDP) ta bayar da kudin da aka saya wa matasan kayayyakin da za su rika gudanar da sana’o’in da suka koya.” Inji shi.
Ya ce matasan da suka koyi sana’o’i yanzu za su daina zaman banza saboda sun samu sana’o’in da za su rike kansu.
Ya bukaci matasan su rike sana’o’in da aka koya musu da muhimmanci kasancewar za su taimake su wajen gudanar da rayuwarsu cikin sauki.
“Mun fara koya wa matasa sana’o’i a jihar Filato ne tun a shekarar 2009, inda muka koyawa da dama. Muna da wuraren koya wa matasa sana’o’i a kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta Kudu da kuma Mikkan.”
Ya bukaci al’ummar Jihar Filato su ci gaba da ba su kungiyarsu hadin kai kan wannan aiki da suka sanya a gaba.
A nata jawabin Daraktar kungiyar Mata Musulmi ta Najeriya reshen Bukur Hajiya Binta Hassan Hussaini ta bayyana matukar farin cikinta da wannan shirin.
Ta ce “Mun dade muna neman irin wannan dama amma ba mu samu ba, sai a wannan lokaci. Babu shakka shirin zai taimaka wa matasanmu wajen samun sana’o’in da za su yi.”
Ta ba matasan da aka koyawa sana’o’i su kasance masu juriya da hakuri wajen rike sana’o’in da aka koya masu, kasancewar yin hakan zai sa su samu gagarumar nasara.
daya daga cikin malaman da suka koyar da matasan Malam Sa’idu Ibrahim ya shawarci matasan kasar nan kada su dogara da aikin gwamnati.
“A yanzu idan gwamnati ta ba mutum aiki ba ta da kudin da za ta biya shi albashi, saboda ta dogara ne da kudin man fetur, kuma a yanzu kasuwar man fetur ta fadi a duniya. Don haka kada matasa su dogara da gwamnati.” Inji shi.
kungiyar Apurima ta koya wa matasa 149 sana’o’i
kungiyar Apurima Onlus tare da hadin gwiwar hukumar bunkasa kasashe ta Majalisar dinkin Duniya (UNDP) ta koya wa matasa 149 sana’o’i da suka hada dinki…