’Yan kungiyar Ansaru da ke ci gaba da mamaye yankunan da ke Gabashin Karamar Hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna sun haramta kowanne irin harkokin siyasa a yankin.
Kungiyar ta dauki matakin ne domin nuna adawarta da tsarin mulkin siyasa ta Dimokuradiya.
- Bankuna sun damfare mu biliyan 22 cikin wata guda – MTN
- Yadda muka ceto almajirai 21 daga coci a Jos – DSS
Batun ya fito ne a cikin wata sanarwa da Kungiyar Ci Gaban Masarautan Birnin Gwari ta BEPU mai dauke da sa hannun shugabanta, Ishaq Usman Kafai .
A cewarsa, a yanzu haka duk yankunan da ke gabashin Birnin Gwari na karkashin ikon yan bindigan ne ta Ansaru.
Ya ce mazabu bakwai daga cikin 11 na Gabashin Karamar Hukumar kuma duk suna a karkashin ikon ’yan Ansarun ne.
A cewar Shugaban na BEPU, a makon jiya ma sai da ’yan Ansaru suka yi wa wani matashi mai sanar acaba duka saboda ganinsa da suka yi da hotan wani dan takara.
Kungiyar ta BEPU at bayyama yankin tsohon Kuyello da Damari da ke mazabar Kazage a matsayin inda ’yan Ansarun ke cin karensu ba babbaka.
“Wannan hali da muka tsinci kanmu na matukar damun mu domin yana nuna ke nan ba mu san yadda zabe mai zuwa zai kasance ba saboda ko zaben Kananan Hukumomin da aka yi a baya ba a gudanar a yankin ba, hakan ya sa tilas aka bayyana zaben da cewa bai kammalu ba.
“Wannan ya sa aka saka mana Shugaban riko a Karamar Hukumar, sannan kuma ’yan bindigar sun ci gaba da kwasar matasa suna shigar da su kungiyar.
“Har ta kai kwanan biyu daga cikin ’yan Ansarun za su angonce da wasu ’yan mata biyu,” inji shi.